1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta hana jirage tashi a Yemen

Abdul-raheem Hassan
November 6, 2017

Tashohin jiragen sama sun daina aiki daga ranar Litinin a yammacin kasar Yemen, a wani mataki na maida martanin harin makami mai linzami da aka harba kusa da birnin Riyadh na Saudiyya.

https://p.dw.com/p/2n6rt
Komoren Flugzeugabsturz
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan mataki ya sa hukumomin sufurin jiragen kasar Yemen suka sanar da soke dukkanin zirga-zirgan jirage a fadin kasar, matakin ya shafi tashoshin jiragen ruwa da na kasa da sauran hanyoyin sufuri na kowani bangare.

Wannan mataki baya rasa nasaba da sanarwar da dakarun kawancen Saudiyya suka fitar na rufe sararin samaniyar biranen Aden da Seyoun da ke yammacin kasar. Sojojin da Saudiyya ke jagoranta ne ke rike da iko a mafi yawancin yankunan da ke yammacin kasarb ta Yemen.

A tun watan Agustan shekara ta 2016, dakarun kawance karkashin jagorancin sojojin Saudiyya suka bada umarnin rufe babban fili jirgin saman kasar Yemen da ke Sanaa, yankin da ke hannun 'yan tawaye.

An sake bude filin jirgin saman Sanaa a YemenI S ta dau alhakin harin Yemen