1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta cafke masu shirin harin tarzoma

Zainab MohammedDecember 23, 2007
https://p.dw.com/p/CfRl

Maaikatar harkokin cikin gida ta kasar Saudi Arabia tace jami’an tsaron ta sun cafke wasu tsageru ,guda daga cikin su baƙi dake shirin kai hare haren ta’addanci a wannan masarauta.To sai dai kawo yanzu babu alakar mutanen da aka cafke da kungiyar alqaida data shirya kai hari lokacin aikin hajji a birnin Mecca. sanarwar data fito daga maaikatar harkokin cikin gidan Saudiyyan na nuni dacewar,tun daga ranar 14 ga wannan wata na Disamkba kawo yanzu,an cafke mutane 28 da ake zargi da alaka da kungiyar ta Alqaeda.A ranar jumaa nedai,maikatar da sanar dacewar wannan kungiya na shirin kai hari birnin Mecca ayayinda ake aikin hajji.