1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSaudiyya

HRW: Saudiyya ta halaka 'yan ci-rani

August 21, 2023

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta ce Saudiyya na gallaza wa 'yan ci-rani daidai lokacin da kasar ke kokarin gyara mutuncinta a duniya.

https://p.dw.com/p/4VOK4
Hoto: Balkis Press/ABACAPRESS/picture alliance

Jami'an tsaron kan iyaka na kasar Saudiyya sun harba makamai masu hatsari ga wasu  'yan ci-rani da ke hankoron shiga kasar ta mashigar kasar Yemen. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ce ta yi zargin hakan a wannan Litinin. Kungiyar ta ce wannan cin zali na jami'an na Saudiyya tuni ya yi ajalin daruruwan 'yan ci-ranin da galibinsu suka fito daga kasar Habasha.

Kawo yanzu hukumomin Saudiyya ba su kai ga mayar da martani ga wannan zargi ba, amma a cikin sanarwa da ta fitar, Nadia Hardman, wata jami'ar kungiyar ta Human Rights Watch, ta ce  bai kamata kudaden da Saudiyya ke kashewa wajen sayen fitattun 'yan wasan kwallon kafa na duniya su dauke hankulan mutane daga wadannan laifuka masu muni da hukumomin Saudiyya ke yi wa dan Adam ba.