1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin matakan tsuke bakin aljihu a Saudiyya

Gazali Abdou Tasawa MNA
May 11, 2020

Gwamnatin Saudiyya ta sanar da kara kudaden harajin fito da kuma janye tallafin iyali a wani mataki na fuskantar matsalar tattalin arzikin da ta shiga a sakamakon annobar COVID-19.

https://p.dw.com/p/3c1yz
Social Distancing Abstand halten in Corona-Zeiten weltweit
Hoto: Reuters/Ahmed Yosri

Kasar Saudiyya da ke zama kasa ta farko a arzikin man fetur a duniya ta sanar a wannan Litinin da daukar wasu sabbin matakan tsuke bakin aljihu domin fuskantar matsalar komabayan tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a sakamakon faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya da kuma annobar Coronavirus.

Matakan tsuke baki aljihun sun hada da nunka gida uku dokar harajin TVA ko VAT ta kan kayakin masarufi da za ta tashi daga kaso biyar cikin dari zuwa 15 cikin 100, da kuma janye kudin tattafi da gwamnati ke bai wa kowane dan kasa.

Matakin janye tallafin zai soma daga watan Yuni da ke tafe a yayin da sabuwar dokar harajin ta VAT za ta soma aiki daga daya ga watan Yuli. Gwamnatin kasar Saudiyyar na sa ran samun kusan miliyan 25 na Euro a karkashin matakin tsuke bakin aljihun wanda amma ake fargabar zai haifar da fushin al'umma a kasar.