1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi a Saudiyya sun fara aikin bana

July 29, 2020

A wannan Larabar ce musulmi suka fara aikin hajjin bana a kasa mai tsarki yayin da aka takaita yawan alhazan sabado annobar corona

https://p.dw.com/p/3g877
Saudi-Arabien Mekka | Corona & Hadsch | Pilgerfahrt
Hoto: Getty Images/AFP

An takaita yawan maniyatan da ke aikin hajjin na bana basu da yawa saboda annobar corona da ta yadu a fadin duniya.

'Yan kasar Saudiyya ne kadai da kuma baki daga kasashe kimanin 160 wadanda ke zaune a kasar ta Saudiyya suke gudanar da aikin hajjin ba bana.

A shekarun baya dai musulmi kimanin miliyan biyu da rabi ke hallara a birnin Makka domin gudanar da aikin hajjin wanda ke zama daya daga cikin shikashikan musulunci guda biyar da ake bukatar dukkan musulmi da ke da iko ya halarta akalla sau daya a rayuwarsa.

Alhazan za su kwana yau a Minna kafin su wuce zuwa hawan Arfat a ranar Alhamis.