1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyara a dokar kananan yara a Saudiyya

Mahamud Yaya Azare LMJ
April 27, 2020

Ana ci gaba da mai da mayar da martini ga matakin mahukuntan Saudiya na soke hukuncin haddin bulala da kisan wadanda suka aikata laifi tun ba su kai shekarun balaga ba.

https://p.dw.com/p/3bTj4
Saudi Arabien Wandbild König Salman bin Abdulaziz  Prinz Mohammed bin Salman
Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Mohammed bin Salman Hoto: Getty Images/AFP/A. Qureshi

Kotun kolin kasar ta Saudiyya ce dai ta wallafa batun gyaran dokar a shafinta na Internet, inda kafofin yada labaran kasar kuma suka ruwaito. Kotun ta bayyana cewa, daga yanzu hukuncin haddin bulala da ake yi da a wasu lokutan yakan kai daruruwan bulalu ya zama tarihi, kana za a maye gurbin hukuncin da tara ko dauri, a wani mataki na kare hakkin dan Adam da kuma aiwatar da sauye-sauyen da ake yi, karkashin kulawar mai martaba sarki Salman  bin Abdul-Azeez da dansa yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman.

Kare hakki ko matsin lamba?

Tun bayan da wata kotu a kasar ta Saudiya, ta zartar da hukuncin bulala dari ga mai fafutukar fadin albarkacin baki na kasar, Raif Badawi a bainar jama'a shekaru biyun da suka gabata, wanda a yanzu haka yake ci gaba da shan dauri kan zargin yin sabo da raina masarautar, kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka kafawa kasar ta Saudiyya kahon zuka kan lallai sai ta soke haddin na bulala.

***SPERRFRIST 24.09.2018 um 09.00 Uhr*****  Right Livelihood Award Abdullah al-Hamid, Mohammad Fahad al-Qahtani und Waleed Abu al-Khair
Abdullah al-hameed a farko Hoto: Right Livelihood Award/Ahmed al-Osaimi

Wannan sabon matakin ma dai na zuwa ne kwanaki uku bayan mutuwar fitaccen dan fafutukar lauyan nan na kasar, Abdullah al-hameed a gidan jarum da ya yi ta fama da jinya a inda yake dauren. Dan shekaru 69, al-hameed jigo ne a kafa kungiyar Hasm da ke fafutukar kafa tafarkin dimukuradiyya a da zai maye gurbin na masarautar da tai kaurin suna wajen mulkin kama karya. Bugu da kari, mahukuntan na Saudiya sun sanar da soke zartar da hukuncin kisa ga wadanda aka yanke wa hukuncin tun ba su kai shekaru 18, da kasar ta amince da su a matsayin shekarun balaga ba, lamarin da ke ci gaba da jawo cece-kuce a kasar.
Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam irin su Amnesty International, ta bakin kakinta Rovert Sharp ta yi fatali da wannan sauyin da ta ce na jeka na yika ne: "Ya zama wajibi ga kasashe da kungiyoyi masu 'yanci na kasa da kasa, su kara matsawa Saudiyya lamba domin ganin ta ci gaba da mutunta hakkin dan Adam.Wadannan sauye sauyen ba za su gamsar ba. Idan da gaske suke, su sako illahirin masu fafutuka maza da mata da ake tsare da su ba tare da sun aikata komai ba, sai tofa albarkacin bakinsu."

Frankreich | Demonstranten von Amnesty International protestieren am Internationalen Frauentag in Paris vor der saudi-arabischen Botschaft
Amnesty International ta bukaci a sako sauran firsinoniHoto: Reuters/File Photo/B. Tessier

Watsar da ra'ayin rikau

Tun bayan da aka ayyana Muhammad bin Salman a matsayin yarima mai jiran gado, ya gabatar da sauye-sauyen da suke nesanta kasar da tsohon tsarinta da aka santa da shi, na bin koyarwar Islama bisa tsarin masu ra'ayin mazan jiya, sauye-sayen da suka kai ga bude gidajen rawa da disko da silima da bai wa mata 'yancin tuki da yawo da shiga gidajen shakatawa, sauye-sauyen da zargin kashe dan jaridar kasar Jamal Khashoggi da ake wa bin Salman da yi, ya bata masa rawarsa da tsalle a wajen kungiyoyin kare hakkin dan Adam.