1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma'aikatan Twitter na yi wa jama'a kutse

Ramatu Garba Baba
November 7, 2019

Masu shigar da kara sun soma tuhumar wasu ma'aikatan kamfanin fasahar Twitter da bisa laifin yi wa gwamnatin Saudiyya leken asiri bayan da aka zargesu da laifin yi wa wasu fitattun mutane kutse.

https://p.dw.com/p/3Sbo9
Twitter
Hoto: picture-alliance/dpa/ZB/M. Skolimowska

Masu shigar da kara sun ce sun gano yadda aka yi hayan wadannan kwararrun kamfanin, domin su yi ta sa ido kan shafukan wasu fitattun mutane da ake ganin na yawan sukar manufofin gwamnati. Sun ambato wani da ke da masu binsa fiye da miliyan daya a Twitter da kuma wani fitacce dan jarida, ba tare da an baiyana sunayensu ba, da aka ce suna daga cikin wadanda Saudiyyan ta bayar da izinin a saka wa ido sosai.