1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

An yi wa shugabannin awaren Kataloniya sassauci

Gazali Abdou Tasawa
July 17, 2020

Gwamnatin yankin Kataloniya a kasar Spain ta sanar da daukar matakin yin sassauci ga jagororin 'yan awaren yankin Kataloniya su tara da ake tsare da su a gidajen kurkuku tun a shekara ta 2017. 

https://p.dw.com/p/3fUb9
Carles Puigdemont Katalonien
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Matthys

Gwamnatin yankin Kataloniya a kasar Spain ta sanar da daukar matakin yin sassauci ga jagororin 'yan awaren yankin Kataloniya su tara da ake tsare da su a gidajen kurkuku tun a shekara ta 2017. 

Matakin sassauci ya tanadi bai wa shugabannin 'yan awaren da ke tsare izinin komawa cikin iyalansu a karshen kowane mako kana su koma kurkukun a kowace Litinin.

 Gwamnatin yankin na Kataloniya ne ta sanar da hakan a wannan Juma'a inda ta ce tuni tun da safiyar wannan litinin aka sallamo mutanen daga gidajen kurkukun da ake tsare da su. Sai dai hukumomin shari'ar yankin na iya kalubalantar mataki a gaban kotun kolin kasar.