1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarkozy na bayan Hollande a zaɓen Faransa

Umar Saleh SalehApril 23, 2012

Francois Hollande da Nicolas Sarkozy za su je zage na biyu a zaɓen shugaban ƙasar Faransa, inda ita kuwa Marine Le Pen ta bada mamaki da ta samu matsayi na uku

https://p.dw.com/p/14iOC
Francois Hollande, Socialist Party candidate for the 2012 French presidential election, attends a campaign rally in Cenon, near Bordeaux April 19, 2012. REUTERS/Stephane Mahe (FRANCE - Tags: POLITICS ELECTIONS)
Präsidentschaftswahlen Frankreich 2012 Francois HollandeHoto: Reuters

A ƙasar Faransa shugaba Sarkozy yasha kaye a zagai farko na zaben shugabancin ƙasar, bisa ga hasashen farko da kamfanin dillacin labaran ƙasar Faransa wato AFP ya bayar, ya nuna cewa ɗan takaran shugaban ƙasa na jam'iyar gurguzu Francois Hollande shine ya yi nasara a zagayen farko wanda aka yi a yau. Alƙaluman farko da aka bayar sun nanu cewa Holande ya samu sama da kashi 28 izuwa cikin ɗari na yawan ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da shuga mai ci Sarkozy ya samu kashi 27 biyar, abinda ke nuna cewa dukan nisu, sun samu nasaran zuwa zagaye na biyu.

Amma dai a zahiri zagayen farko Sakozy yasha ƙasa. Ita kuwa Marine Le Pen ta samu kashi 18 cikin ɗari na yawan ƙuri'un abinda aza ta matsayi na ukku a zaɓen. Yanzu haka dai ana ta hasashen shugaba Sarkozy zai sha kaye koda a zagaye na biyu, abinda kuma zai sa ya kafa tarin´hin kasancewa shugaban da ya yi wa'adi ɗaya a shugabancin ƙasar Faransa tun sa ma da shekaru 30. An dai bayyana cewa sama da kashi 80 na masu kaɗa kuri'a suka fito a zaɓen.

French President Nicolas Sarkozy listens to speeches during his visit at Brie-Comte-Robert hospital, some 30km east of Paris, France, 06 July 2010. Sarkozy rejected 06 July allegations that he and his party treasurer received illegal campaign donations, branding them political smears. An accountant, identified by the investigative website Mediapart as Claire T., said Eric Woerth, a Sarkozy ally and treasurer of his UMP party, received the donation in March 2007, ahead of Sarkozy's election victory in May. EPA/YOAN VALAT
Nicolas Sarkozy, wanda ya fadi a zagayen farko na zaben FaransaHoto: picture alliance / dpa

Gabanin zaɓe

Duk da yanayi na tsananin sanyi da iska da ake fama da shi dai dubban mutane magoya bayan Sarkozy ne suka dafifi zuwa cibiyar birnin Paris, domin sauraron jawabin yakin neman zaɓe zagaye na biyu na shugaba Nicolas Sarkozy. Waɗannan magoya baya dai sun fito ne domin karfafa wa shugaban kasar gwiwa, kamar yadda Lorine mai shekaru 21kuma daliba mai nazarin ilimin shari'a ta nunar.

Ta ce " akwai sarkakiya dangane da wannan zagayen zaben, amma mun yi imanin cewar Sarkozy zai samu nasara. kasancewar manufofin shi ta fannin tattalin arzikin kasa sun fi na abokin takararsa, kuma munga irin rawa daya taka lokacin tattalin arzikin faransa ya shiga mawuyacin halai. Wannan shine abun da mutanen faransa ke la'akari akai. Amma ina ganin zai cimma nasara".

Francois dake zama wani tsohon ma'akacin hukumar kashe gobara a Faransa, wanda ya yi tattaki daga yankin kudancin kasar zuwa birinin Paris domin halartan gangamin yakin neman zaben na shugaban kasa zagaye na biyu.

Patricia bata kasance wata mai bada goyon baya ga shugaban kasar ba. Mai shekaru 51 da haihuwa, ta kasance tamkar 'yar kallo ce kawai na dubban mutanen da suka yi dafifi domin halartan jawabin Sarkozy a yakin neman sake neman zabensa..

France's far right presidential candidate and National Front party President Marine Le Pen delivers a speech at a political rally in Marseille March 4, 2012. REUTERS/Philippe Laurenson (FRANCE - Tags: POLITICS)
Wanda ta zo na uku a zaben shugabacin kasar Faransa, Marine Le PenHoto: Reuters

Tace "tsawon awa guda kenan nake zaune a kan wannan gadar. Yawancin mutanen da nake gani suna kwarara masu shekaru daga 50 zuwa 70 ne. Ban hangi matasa ba, sai 'yan Afrika kalilan, kuma babu larabawa. Hakan na nuni dacewar, wani rukuni na al'umma kadai ke goyon bayansa. Amma kuma babu yadda mutun zai shugabanci wani rukuni kalilan na al'umma".

Patricia dai na ganin cewar shugaba Sarkozy zai sha kaye. Sai dai duk da haka zasu bashi kuri'unsu, saboda suna jiwa kudadensu tsoro.

Hasashe kan Sarkozy

Jawabin shugaba Nicolas Sarkozy bai mayar da hankali kan magoya bayansa kadai ba, amma zuwa ga al'ummar Faransa baki daya. Yayi magana kai tsaye ga wadanda basu da karfi cikin al'umm, rukunin mutanen da suka fi jin radadin matsalar tattalin arziki. Yayi gargadi dangane da zaɓen jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi. Kazalika yayi alkawarin kaddamar da tsauraran wuraren bincike ta kan iyakokin Faransa, tare da karfafa tsarin tattalin arzki.

Sarkozy yace "matsalar kan iyakoki ba zai zame batun kadai ba, amma zan kaddamar da mahawara a babban bankin Turai dangane da irin matakai da yake dauka domin bunkasar tattalin arziki. Domin Idan Bankin bai bada goyon baya ba, ba za mu samu ingantaccen bunkasar tattalin arziki ba".

French candidate for the 2011 Socialist party primary elections Francois Hollande, left, waves after the Party announced his victory during the second round of the Socialist Party's primary vote, in Paris, Sunday Oct. 16, 2011. France's Socialists and sympathizers on Sunday are choosing their nominee for next year's presidential election, an expected showdown with embattled conservative President Nicolas Sarkozy.(Foto:Thibault Camus/AP/dapd)
Francois Hollande wanda yazo na faro a zaben FaransaHoto: dapd

Sarkozy dai ya tabbatarwa da al'ummar kasar cewar shine kadai mutuminda zai iya kai Faransa tudun mu tsira , tare da kammala jawabin nasa da kira zuwa ga masu kada kuri'a..

" kada ku tsorata al'ummar Faransa, kada kuji tsoron cewar wasu zasu faɗi sakamakon kun biya bukatunku. Mutanen faransa ku saurari roko na, ku taimaka min. Allah ya albarkaci wannan al'umma, Allah Ya daukaka Faransa".

Sakakamon jin kuri'a na jama'a na nuni da cear abokin takararsa Francois Hollande na dada samun karin magoya baya, batu dake kara sanya Sarkozy cikin wani yanayi na tsaka mai wuya a zabukan 22 ga watan Afrilu da 6 ga watan Mayu mai kamawa.

Manufofin Hollande ga Al'umma

Francois Hollande, kamar yadda ake ji daga matasan jam'iyar ta gurguzu, ana daukar sa a matsayin dake iya cika burin jam'iyar na kayar da shugaba mai ci, Nicoas Sarkozy a zaben, amma ba mutum ne da ya shiga zukatan yan gurguzu kamar yadda Segolene Royal tayi shekaru biyar da suka wuce ba. Shi kansa dan takarar yakan kwatanta kansa ne a matsayin mutum mai saukin kai da son zuciya ko nuna shi wnai ne. A daura da haka, ra'ayoyin jama'a da aka dauka, sun tabbatar da cewar shugaba mai ci, Nicolas Sarkozy ba'a taba samun shugaban kasa a Faransa da bashi da farin jini kamar sa ba.

French President Nicolas Sarkozy pauses before answering questions during a media conference at an EU summit in Brussels on Friday, Dec. 9, 2011. European leaders are wrestling over how much of their sovereignty they are willing to give up in a desperate attempt to save the ambitious project of continental unity that grew from the ashes of World War II. At stake at the summit in Brussels, which began Thursday evening, is not only the future of the euro, but also the stability of the global financial system and the balance of power in Europe. (AP Photo/Michel Euler)
Nicolas Sarkozy, wanda ya fadi a zagayen farko na zaben FaransaHoto: dapd

Masana al'amuran zabe suka ce wadanda suka ki jefawa Sarkozy kuri'un su a ranar zabe ba tilas bane su jefawa Hollande. Musmaman shima shugaban jam'iyar masu neman canji, Jean Luc Melenchon, wada yace yana da hanyoyi masu sauki na tsao Faransa daga matsalolin da take fama dasu yanzu, yana iya janye kuri'u masu yawa daga yan gurguzun.

Francois Hollande dan hekaru 57 da haihuwa, a fagen siyasa sannu a hankali ne, tareda aiki tukuru ya kai matsayin da yake a yanzu. Lokacin da Faransawa a shekara ta 1981 suka zabi Francois Mitterand karo na arshe a matsayin sugaban kasa dan gurguzu, Holland yana da shekaru 26 da haihuwa an tura shi wani lardi inda daga can ne ya likkafar sa tayi gaba, ko da shike da farko bai sami galaba a takarar da yayi da Jacques Chira ba, wadda daga baya shima ya zama shugaban Faransa.

Dan takarar na jam'iyar gurguzu yace yayi wa Faransa alkawura masu tarin yawa, wadanda idan har yaci zabe kuma bai aiwatar dasu ba, sakamakon da zai biyo baya zai zama mai muni ga kasar tsawon shekaru masu yawa nan gaba.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita : Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani