1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Salman ya amince ministoci su yi taro ko da baya nan

August 8, 2024

Sarki Salman na Saudiyya ya ayyana sabuwar doka da ta amince ministocin kasar su gudanar da taron majalisar zartaswa ko da kuwa da shi da dansa Yarima Mohammed bin Salman wanda ke rike da mukamin firaminista ba sa nan.

https://p.dw.com/p/4jGWz
Hoto: Courtesy of Bandar Algaloud/Saudi Royal Court/REUTERS

Sarkin na Saudiyya mai shekaru 88 na fama da rashin lafiya, inda a watan Mayun da ya gabata aka yi masa aiki na musamman a huhunsa, lamarin da ya tilasta wa Yariman Mohammed Salman dage ziyarar aikin da ya so kai wa kasar Japan.

Yariman Mohammed bin Salman mai shekaru 38 ne dai ke tafiyar da kusan manyan al'amura na shugabancin Saudiyya tun daga shekara ta 2017, lokacin da mahaifinsa ya ayyana shi a matsayin magajinsa.

A shekara ta 2022 ne kuma, sarkin na Saudiyya ya nada dan nasa mukamin firaminista, lamarin da ya kara wa matashin karfin ikon juya akalar kasar mafi karfin arzikin mai a duniya.