1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Charles na III ya fara ziyara a Jamus

Ahmed Salisu
March 29, 2023

Sarki Charles na III na Birtaniya ya iso nan Tarayyar Jamus don fara ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku, inda zai gana da shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz da sauran kusoshin gwamnati.

https://p.dw.com/p/4PRrY
Großbritannien | King Charles III in Bolton
Sarki Charles na III na Birtaniya tare da mai dakinsa Sarauniya CamillaHoto: Ed Sykes/REUTERS

 

Dazu da rana ne dai jigin Sarkin ya sauka a birnin Berlin tare da mai dakinsa Sarauniya Camilla, kana daga bisani suka zarce zuwa kofar nan ta Brandenburg da ke tsakiyar birnin na Berlin don shaida tarba ta alfarma da kuma macin soja da aka shirya masa.

Yayin ziayarar dai, Sarkin zai yi jawabi ga majalisar dokokin kasar, wanda shi ne irinsa na farko da wani basaraken Birtaniya zai yi, sannan zai gana da 'yan gudun hijirar na kasar Ukraine da suka kauracewa kasarsu sakamakon yakin da Rasha ke yi a kasar.

Wannan ziyarar tasa dai ita ce irinta ta farko da ya kai wata kasa tun bayan da ya dare kan gadon mulkin Birtaniya din, biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth wadda ta rasu a watan Satumbar shekarar da ta gabata.