1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarki Abdallah na kasar Saudiyya na ya da zango yau a kasar Malesiya, a ci gaba da rangadin da yake kai wa wasu kasashen Asiya.

January 30, 2006
https://p.dw.com/p/BvAE

Sarki Abdullah na kasar Saudiyya, ya sauka a birnin Kuala Lumpur na kasar Malesiya yau, a ci gaba da ziyarar aiki da yake kai wa wasu kasashen Asiya. Rahotannin da suka iso mana sun ce sarkin zai yi shawarwari da mahukuntan Malesiyan ne a kan hanyoyin inganta kwarjinin duniyar musulmi a fagen siyasar kasa da kasa da kuma matakan da za a dauka wajen kau da yaduwar akidar `yan tsageru. kololuwar ziyarar sarki Abdullah ta yini uku a kasar, za ta kasance ne ganawar da zai yi gobe talata da Firamiya Abdullah Ahmad Badawi na Malesiyan, wanda kuma a halin yanzu shi ne ke shugabancin kungiyar Muslmi ta Duniya.

A cikin wata fira da ya yi da maneman labarai, a gun bikin yi wa sarki Abdullah marhaba gaban Majalisar edokokin kasar, ministan harkokin wajen Malesiyan Sayed Hamid Albar, ya bayyana cewa Saudiyya da kasarsa na matukar aikin hadin gwiwa wajen inganta irilin addinin islama, da bunkasa shirye-shiryen kungiyar Musulmi Ta Duniya da kuma cim ma hadin kan al’umman musulmi a duniya baki daya.

Wannan dai shi ne karo na farko tun shekarar 1970, da wani sarkin kasar Saudiyya ya taba kai ziyara a Malesiyan, kasar da ke bin sassaucin ra’ayi kuma mai rinjayin musulmi a tsarin al’ummanta.