1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanya Idanu kan rikicin Siriya

April 23, 2012

Masu sanya idanun da Majalisar Ɗinkin Duniya ta tura don sa ido kan shirin zaman lafiya a Ƙasar Siriya sun fara rangadi a yankunan da ke kusa da Damascus, babban birnin ƙasar ta Syria.

https://p.dw.com/p/14jfJ
Syrian refugees and local residents take part in a demonstration against Syria's President Bashar Al-Assad, after Friday prayers outside the Syrian embassy in Amman April 6, 2012. REUTERS/Ali Jarekji (JORDAN - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Mai magana da yawun masu sanya idanun Neeraj Singh ya bayyana cewar masu sanya idanun za su zazzagaya yankunan da nufin tabbatar da cewar shirin zaman lafiyar da ya fara aiki ranar sha biyu ga wannan da mu ke ciki ya ɗore.

Mr. Singh ya ƙara da cewar baya ga waɗanda a yanzu haka ke gudanar aikin sanya idanun kan shirin na tsagaita wuta tsakanin dakarun shugaba Assad da na waɗanda ke rajin kawar da shi daga karagar mulki, ana sa ran isar masu sanya idanu talatin nan da 'yan kwanaki, gabannin isar ƙarin wasu ɗari uku da Kwamitin Sulhu na Majlaisar Ɗinki Duniya zai aike.

To sai dai duk da isar masu sanya idanun da ma dai fara aiki da shirin tsagaita wutar, a ƙarshen makon da mu ka yi bakwana da shi an tafka fada a wasu yankunan wanda hakan ya yi sanadiyar asarar rayukan mutane ashirin da takwas.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Abdullahi Tanko Bala