1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanarwar gwamnatin Jamus akan matsalar takardun kuɗin Euro

December 2, 2011

A sanarwar gwamnatinta da ta bayar, Angela Merkel ta ce wajibi ne a yi wa yarjeniyoyin gamayyar takardun kuɗi Euro kwaskwarima domin hana gamayyar tabarɓarewa kwata-kwata

https://p.dw.com/p/13LiP
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: dapd

Mako ɗaya kafin taron ƙolin shugabannin ƙungiyar tarayyar Turai a Brussels, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ba da sanarwar gwamnatinta akan mahawarar da ake tafkawa dangane da matsalar bashin dake addabar kasashen Turai, inda ta nuna cewar har yau dai tana kan bakarta a game da yi wa yarjeniyoyin hadin kan Turai kwaskwarima a fafutukar shawo kan matsalar takardun kuɗin Euro

Ƙasashen Turai na fama da wata mummunar matsala mafi tsanani irinta da suka taɓa fuskanta tun bayan gabatar da takardun kuɗin Euro, wataƙila ma dai tun bayan gabatar da matakan haɗin kan Turai. Wannan bayanin an ji shi ne daga bakin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel mako ɗaya kafin taron ƙolin shugabannin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai a Brussels. Musabbabin wannan matsalar shi ne bashin da ya kai wa wasu ƙasashen ƙungiyar iya wuya da kuma rashin wani angizo a gasar ciniki ta ƙasa da ƙasa. Wannan maganar babu wata rufa-rufa game da ita. Kazalika illahirin ƙasashen sun haƙiƙance cewar tilas ne a tinkari wannan mummunan ci gaba tun kafin matsalar ta zama gagara-badau. Sai dai kuma hakan ba zata samu a cikin ƙiftawa da gani ba:

"Gwamnatin tarayya ta sha nanata cewar ba za a iya shawo kan matsalar basussukan ƙasashen Turai nan take ba. Abu ne dake buƙatar lokaci kuma wajibi ne a bi shi sannu a hankali."

500 Euro Schein, Euro
Takardar Euro dari biyarHoto: EZB

An dai samu ci gaba sosa a fafutukar shawo kan matsalar da ake fama da ita. An gabatar da shawarar kafa wata gamayyar daidaita darajar takardun kuɗi, wadda zata taimaka wajen ƙarfafa makomar gamayyar tattalin arziƙi da haɗin kan takardun kuɗi ta ƙasashen Turai. Amma wannan gamayyar ba zata cimma nasara ba face idan an yi kwaskwarima ga yarjeniyoyin Turai tare da daukar matakan takunkumi na kai tsaye akan ƙasashen gamayyar dake da laifukan giɓin kasafin kuɗi. A ranar litinin mai zuwa Jamus da Faransa zasu zayyana wasu shawarwari na haɗin guiwa, waɗanda zasu gabatar a zauren taron ƙolin na Brussels. Amma zargin da ake wa Jamus na neman yin babakere a al'amuran Turai, abu ne da ba ya da madogara in ji Angela Merkel:

"Muna goyan baya wani takamaiman tsari na tabbatar da darajar takardun kuɗi da daidaituwar al'amuran tattalin arziƙi, bisa aƙidar haɗin kan Turai ta Konrad Adenauer da Helmut Kohl. Jamus da sauran ƙasashen Turai duk jirgi ɗaya ne ke ɗauke da su, kuma ba zamu taɓa mantawa da hakan ba."

To sai dai kuma shugabar gwamnatin ta Jamus ta fuskanci suka da kakkausan harshe akan wannan matsayin da ta ɗaukan daga 'yan hamayya, musamman ma daga Jürgen Tritten, kakakin 'yan the Greens a majalisar dokoki, wanda ya ce tuni aka ɗora wa kowa-da-kowa alhakin matsalar bashin. Ya ba da shawarar kafa wani asusun biyan basusukan kasashen Turai da kuma lasin na banki ga asusun taijmako na ƙasashen dake amfani da takardun kuɗin Euro. Shi kuwa kakakin 'yan Social-Democrats Frank-Walter Steinmeier ya zargi Merkel ne da ƙara rura wutar rikicin takardun kuɗin Euro:

Frank-Walter Steinmeier SPD Fraktionschef
Kakakin SPD a majalisar dokoki Frank-Walter SteinmeierHoto: dapd

"Rikicin Turai ya daɗa yin tsamari kuma ke Merkel da gwamnatinki, ko da yake ba ku ne kuka haddasa rikicin ba, amma take-takenku shi ne ya taimaka matsalar ta kai intaha inda a yanzu ake fama da taɓarɓarewar tattalin arziƙin Turai. Wannan gwamnati ta haɗin guiwa dake fama da rashin haɗin kai tana barazana ga daidaituwar tattalin arziƙin Turai. Wannan shi ne gaskiyar abin dake akwai."

To sai dai kuma duk da wannan korafi da 'yan hamayyar suka yi, amma a kasuwannin hada-hadar hannayyen jari an yi marhabin lale da sanarwar da ta bayar, inda nan take farashin hannayyen jari yayi sama a Frankfurt da ma sauran sassa na duniya.

Mawallafi: Bettina Marx/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar