1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samame kan AC da Inter Milan

Usman Shehu Usman
September 30, 2024

'Yan sanda a kasar Italiya sun tsare gwamman magoya bayan AC Milan da na Inter Milan lamarin da ya faru a wani gagarumin samamai da 'yan sanda suka kai a sansanonin kungiyoyin kwallon kafan kasar

https://p.dw.com/p/4lFfK
Verhaftung von Mafia Boss Matteo Messina Denaro
Hoto: Carabinieri/REUTERS

Nan take dai a cewar 'yan sanda suka tsare mutane 13, yayinda aka kewaye gidajen wasu karin mutane daga cikin magoya bayan wadannan fitattun kulob din kwallon kafa na duniya. Daga cikin laifukan da ake tuhumar mutnanen da aikatawa sun yi gumbiya-gumbiya wajen sayar da tikiten shiga wasanni, haka kuma sun yi dabaru wajen sayarwa masu son ajiye motocinsu kusa da filin wasanni, haka kuma 'yan mafiyan na Inter Milan da AC Milan ana tuhumarsu da karban kudi a wajen kamfanoni masu yin talla a filayen wasanni, kuma duk sun yi hakanne ta haramtattun hanyoyi. Hukumomin kasar Italiya, suka ce akwai magoya bayan kulob din biyu da yawa wadanda ke cikin kungiyoyin 'yan mafiya.