1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samame a Sina'i ya janyo mutuwar 'yan bindiga-dadi 32

September 8, 2012

Yankin Sina'i na kudancin kasar Masar ya zama wani filin da'ga tsakanin dakarun kasar da 'yan bindiga-dadi.

https://p.dw.com/p/165UW
A boy walks near army trucks carrying tanks and vehicles, expecting opposition against militants, arriving at Rafah city, some 350 km (217 miles) northeast of Cairo August 9, 2012 .Egyptian police fought gunmen in northern Sinai's main town of al-Arish on Thursday, state television reported, a day after security forces began a crackdown on Islamist militants in the region. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST TRANSPORT MILITARY)
Hoto: Reuters

A wani matakin samar da doka da oda a yankin Sina'i da ke fuskantar kalubalen 'yan bindiga dadi a kasar Masar, hukumomin kasar sun dauki matakin farautar ko ta wane hali 'yan bindigar da ke cin karensu ba babbaka a yankin inda a ke da karancin sha'anin tsaro. Wata sanarwar da kakakin rundunar tsaron kasar kanar Ahmed Mohammed Ali ya karanto, ya ce tun bayan harin kwantan baunar da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar 16 a farkon watan da ya shige, hukumomi sun dauki matakin farautar duk wasu 'yan bindiga da ke yankin na Sina'i a kudanci inda a daren Jumma'a ya zuwa safiyar Asabar sojojin kasar suka kashe a kalla mutune 32 yayinda suka cafke 13. To saidai masu lura da al'amuran yankin na cewar dakile matsalar a wannan yankin, sai Allah. A makon da ya gabata ne kasar Isra'ila ta kira ga hukumomin Masar da su janye dakarun nasu kai tsaye a wannan yankin da Majalisar Dinkin Duniya ta hana ajiye dimbin dakaru a cikinsa tun bayan yakin da aka gobza tsakanin kasashen biyu a shekara ta 1979.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Saleh Umar Saleh