1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salwantar rayukan masu zanga-zanga a Masar

February 3, 2011

Waɗanda ke goyon bayan shugaba Hosni Mubarak sun harbe biyu daga cikin masu ƙin jinin gwamnati a wannan alhamis a birnin alƙahira.

https://p.dw.com/p/109hD
Lokacin da sojoji ke tarwatsa masu zanga-zanga a AlƙahiraHoto: AP

Mutane biyu sun rasa rayukansu a dandalin Tahir na birnin Alƙahira, a lokacin da waɗanda ke goyon bayan shugaba Hosni Mubarak suka buɗe wuta a kan gungun mutanen da ke zangar zangar ƙin jinin gwamnati. Wannan kuwa ya zo ne kwana guda bayan salwantar rayukan mutane uku, tare da jikata wasu sama da ɗari a ɗauki ba daɗi da aka fiskanta tsakanin waɗanda ke mara wa shugaba Mubarak baya da kuma waɗanda ke neman ya sauka daga karagar mulki. Tun da jijjiɓin safiyar wannan alhamis ne aka fara fiskantar harbe-harben bindigogi daga gadar da magoyan bayan Mubarak suka kafa zango.

Sai dai tashar talabijin ta Al-arabiya ta ruwaito cewa mace-macen ya biyo bayan harbe-harben kan mai uwa da wabi da sojoji ke yi, da nufin tarwatsa taho mu gama da ɓangarorin da ke gaba da juna ke niyar gudanarwa. Gwamnatin Amirka da ta yi Allah wadai da abin da ke faruwa, tare da tura da jirgi birnin alƙahira domin kwashe duk 'yan ƙasarta da ke da zama a Masar sakamakon taɓarɓarewan harkokin tsaro da ake fiskanta. Duk da alƙawarin da shugaba Mubarak yayi na janye takarar sa a zaɓen watan satumba mai zuwa, masu boren na daɗa jan daga domin tilasa wa shugaba sauka daga karagar mulki.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu