Salwantar rayuka a harin kudancin Yemen
August 5, 2012Wani harin kunar bakin wake da aka kaddamar a wani gari da ke cikin lardin Abyan na kudancin Yemen ya haddasa asarar rayukan mutane 42 tare da jikata wasu sama da 37. Hukumomin birnin Sana'a suka ce wannan harin ya faru ne lokacin jana'izar wani mutum da ke da alaka da sojojin sa kai, da suka taimaka wa dakarun gwamnatin yaki da ayyukan ta'addci na kungiyar Al-Qa'ida.
Ana dai danganta wannan danyen aikin da ramuwar gayya daga bangaren Al-Kaida, wanda ya zo sa'o'i kalilan bayan nasarar hallaka mutane biyar da ake kyautata zato masu kishin addinin musulunci ne da sojojin gwamnati suka yi. Tun dai a farkon wannan shekarar ta 2012 ne gwamnatin Yemen ta sa kafar wando guda da masu tsattsauran ra'ayin addinin musulunci inda ta far musu a lardin da taimakon mayakan sa kai na kabilun Abyan, tare da nasarar mayar da lardin karkashin ikonta.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala