1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fara sako kananan yara a Sudan ta Kudu

Lateefa Mustapha Ja'afarMarch 22, 2015

Asusun Kula da Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya "UNICEF" ya sanar da cewa 'yan tawayen Sudan ta Kudu sun sako wasu kananan yara 250 da suka tilastawa shiga aikin soja.

https://p.dw.com/p/1EvJr
Yaran da ake tilastawa aikin soja a Sudan ta Kudu
Yaran da ake tilastawa aikin soja a Sudan ta KuduHoto: AFP/Getty Images/Ch. Lomodong

Asusun na UNICEF ya ce cikin wadanda 'yan tawayen suka sako har da wata yarinya mai kimanin shekaru tara da haihuwa. Ya kara da cewa duk da ya ke ya yi maraba da farin ciki da wannan ci gaban da aka samu, sai dai har kawo yanzu akwai fargaba mai tarin yawa ganin cewa akwai wasu dubban kananan yaran da ake basu horo a matsayin sojoji a hannun 'yan tawayen. Ana sa ran 'yan tawayen na Sudan ta Kudu za su sako wasu kananan yaran kimanin 400 a cikin makwanni biyu masu zuwa. Rikici dai ya barke a jaririyar kasar ta duniya a shekara ta 2013 tsakanin magoya bayan shugaban kasar Salva Kiir da kuma na tsohon mataimakinsa Riek Machar inda ya yayi sanadiyyar mutuwar dubban 'yan kasar tare da tilastawa wasu kimanin miliyan biyu barin gidajensu yayin da wasu kimanin miliyan hudu ke fama da matsananciyar yunwa.