1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Matakin sake gina Ukraine

Suleiman Babayo MA
June 21, 2023

Taron zai mayar da hankali kan rawar da kamfanoni masu zaman kansu za su taka wajen sake gina kasar Ukraine wadda take karkashin kutsen Rasha fiye da shekara guda da ta gabata.

https://p.dw.com/p/4Ss1y
Yakin Ukraine | Kai hari cikin Ukraine
Ukraine karkashin farmakiHoto: Alina Smutko/REUTERS

A wannan Laraba a birnin London na kasar Birtaniya ake fara taron kwanaki biyu kan matakan sake gina kasar Ukraine. Fiye da wakilai 1000 na gwamnati kasashe 61 gami da masu zuba jari da kamfanoni masu zaman kansu ake sa ran za su halarci zaman taron.

Annalena Baerbock ministar harkokin wajen Jamus gami Svenja Schulze ministar kula da raya kasashe za su wakilci Jamus a wajen taron. Ana kuma sa ran Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine zai shiga zauren taron ta hanyar kafar bidiyo. Taron zai mayar da hankali kan hanyoyin da kamfanoni masu zaman kansu za su zuba jari a kasar ta Ukraine wadda take karkashin farmaki daga Rasha.