1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren NATO ya kai ziyarar bazata a Libya

October 31, 2011

Babban magatakardan ƙungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya kai ziyarar bazata birnin Tripoli na Libya, a daidai lokacin da ƙungiyar za ta kawo ƙarshen hare-haren da ta shafe watannin bakwai ta na kaiwa a Libya.

https://p.dw.com/p/132MA
Secretaren NATO Anders Fogh RasmussenHoto: dapd

Sakatare Janar na ƙungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya kai ziyarar bazata birnin Tripoli na Libya, a daidai lokacin da dakarun ƙungiyar ke shirin tattara na su ya na su su fice daga wannan ƙasa. Wannan dai shi ne karon farko da Rasmussen ya yi tattaki i zuwa Libya tun bayan ƙaddamar da yaƙi da NATO ko OTAN ta yi akan gwamnatin Moammar Gadhafi watannin bakwai ke nan da suka gabata. Haka zalika ziyarar ta zo ne kwanaki uku bayan da ƙungiyar ta NATO ko OTAN ta sanar da janye dakarunta daga yaƙin da ƙasashe 28 suka shiga a dama da su; wanda ya kawar da kanar GadhAfi daga mulki tare da yi masa kisar gilla.

A lokacin da ya ke bayani ga manaima labarai a cikin jirgin soje sanfurin C130 da ya kaishi Tripoli, Rasmussen ya ce da misalin karfe 12 na daren wannan litinin ne, aikin ƙungiyar na kare fararen hulan Libya za ƙare. Ita dai ƙungiyar tsaro ta NATO ta yi amfani da wasu ƙudurori biyu da Majalisar Ɗinkin Duniya ta albarkanta domin afkawa Libya da yaƙi da sunan kare fararen hula.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halimatu Abbas