1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sakataren harkokin wajen Amurka zai je Gabas ta Tsakiya

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
January 4, 2024

Amurka ta ce ba ta fatan ganin yakin ya sake fantsama zuwa sauran sassan Gabas ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/4aqe8
Hoto: Saul Loeb/AP/picture alliance

A wannan Alhamis ce sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke fara wata ziyarar aiki a Gabas ta Tsakiya, irin ta ta hudu tun bayan fara yakin Gaza, a wani mataki na dakile rincabewar yakin zuwa na yankin baki-daya.

Karin bayani:Blinken ya kammala ziyara a Gabas ta Tsakiya da Asiya

Kamfanin dillancin labaran Fmai magana da yawun sakataren harkokin wajen na Amurka Matthew Miller na cewa Amurkar da ma duniya ba sa fatan ganin yakin ya sake fantsama zuwa sauran sassan Gabas ta Tsakiyaaransa AFP ya rawaito .

Karin bayani:Blinken na ci gaba da ziyara a Chaina

Mr Blinken zai fara yada zango ne a Isra'ila wadda ita ce ziyararsa ta biyar a kasar tun bayan fara yakin Gaza, a daidai lokacin da wani hari da ake kyautata zaton na Isra'ila ya hallaka mataimakin shugaban Hamas Saleh al-Arouri a Beirut babban birnin Lebanon, sannan kuma tashin wasu tagwayen bama-bamai a Iran ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100 a Larabar nan.