Sakamakon Zaben Kosovo
October 25, 2004Babu dai wani abin mamaki a game da sakamakon zaben na lardin Kosovo, wanda in da a wasu yankunan duniya ne dabam za a kwatanta shi tamkar wata alama ta zaman lafiya da kwanciyar hankali. Amma a can Kosovo lamarin ya banbanta. Dalili kuwa shi ne mummunar barakar dake akwai tsakanin kabilun lardin. A misalin shekaru biyu da rabin da suka wuce Kimanin kashi 50% na Serbiyawan dake da ikon kada kuri’a suka yi amfani da wannan dama, amma a wannan karon duk illahirinsu suka bijire wa zaben. Wannan matakin na nunarwa ne a fili cewar Serbiyawan na biyayya sau da kafa ga shuagabanninsu, kamar P/M Voyislav Kostunica, da suka yi kiran kaurace wa zaben. Kazalika hakan na mai yin nuni ne da cewar su kansu Serbiyawan na Kosovo ba su ankara da mawuyacin hali na kaka-nika-yi da zasu iya samun kansu a ciki ba. Shi dai Ibrahim Rugova ba zai yarda yayi mulkin hadin guiwa da Serbiyawan da suka kama kashi 10% a majalisar lardin Kosovo ba, saboda ba su da goyan baya ko da na kashi 1% na al’umar lardin. Wannan maganar, ko shakka babu, za a mayar da hankali kanta, lokacin da za a gabatar da shawarwarin ba wa lardin ikon cin gashin kansa, a shekara mai zuwa. Domin kuwa ba wanda zai yarda ya shiga shawartawa da wani mutumin da ba ya da wani tasiri. Tare da wannan mataki na bijire wa zaben Serbiyawan Kosovo suka mika kai bori ya hau ga fadar mulki ta Belgrade, wacce kawo yanzun ta kasa tabuka kome domin kyautata makomar rayuwarsu a wannan lardi. Shi kansa P/M Kostunica, babu wani abin a zo a ganin da zai tsinana musu a lokacin shawarwarin ba wa Kosovo ikon cin gashin kai. Akwai kwararan alamomin dake tabbatar da cewar majalisar dinkin duniya dake wa lardin rikon amana, sannu a hankali, zata ba shi cikakken ikon cin gashin kansa, kuma duka-duka abin da Kostunica zai iya cimmawa shi ne ballewar arewacin Kosovo, wanda ba zai tsinana kome ga makomar sauran sassan da Serbiyawan suka yadu a cikinsu a wannan lardin ba. Amma ga alamu zai ba da goyan baya ne ga kasancewar lardin a dunkule ba tare da canza iyakokinsa ba. Ko kuma a kai ga kirkiro wani tsarin mulki na tarayyar da zai hada Serbiya da Montenegro da kuma Kosovon karkashin laima daya. Bijirewar Serbiyawan tamkar gobarar titi ce ga Albaniyawa, wadanda zasu iya ikirarin cewar babu wani abin dake ci wa Serbiyawan tuwo a kwarya a game da makomar Kosovo. A kuma halin da ake ciki yanzun ba a hangen kyautatuwar al’amuran rayuwa a Kosovo, inda illahirin jami’an siyasar Albaniyawan ke dora alhakin matsalolin da ake fama da su akan hukumar rikon kwarya ta MDD da kuma sojan kiyaye zaman lafiya na KFOR.