1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon taron London akan Libiya

March 29, 2011

Baki ya zo ɗaya tsakanin mahalarta taron duniya akan ƙasar Libiya a birnin London cewar wajibi ne a samu canjin gwamnati a ƙasar ta arewacin Afirka

https://p.dw.com/p/10jpz
Dandalin taron Libiya a LondonHoto: AP

A Talatar nan ne dai fiye da ƙasashen duniya 35 suka gudanar da wani taro a birnin London domin samar da alƙibila akan rikicin dake faruwa a ƙasar Libya sai dai ƙasashen sun lashi takobin ci gaba da kai harin soji a kan shugaba Mouammar Ghaddafi har sai ya dakatar da kisan gillar da suka ce yana yi wa farar hular ƙasar.

Mahalarta taron dai sun haɗa da babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon da takwararsa na ƙungiyar ƙawance ta Nato Anders Fogh Rasmunseen da fraministan ƙasar Qatar da kuma ministocin harkokin waje na ƙasashen duniya kusan 40. A yayin da yake buɗe taron da jawabinsa mai masaukin baƙi fraministan ƙasar Britaniya David Cameron ya ce duk da cewar harin sojin da ake kai´wa sojin Shugaba Ghaddafi yayi tasiri wajen karya lagon Ghaddfi tare da kare fararen hular ƙasar, amma dai har yanzu birnin Misrata yana fama da ƙazamin hari daga sojojin Ghaddafi. Dan haka ina neman wannan taro ya samar da wani kwamiti na tuntuɓa wanda zai ɗora ƙasar Libya bisa gwadabe na siyasa tare da bayar da agaji mai ɗorewa ga al'ummar ƙasar ya kuma ƙara da cewar:

Schweiz Wirtschaft Weltwirtschaftsforum in Davos Großbritannien David Cameron
Piraministan Birtaniya David CameronHoto: dapd

"Mun taru gaba Dayan mu a yau ne saboda dalili guda wanda shi ne agaji ga al'ummar Libya a lokacin da suke tsaka da bukatarsa, na yi imanin cewa yau ya kamata a gabatar da wani matakin da zai baiwa al'ummar ƙasar Libiya damar zaben makomarsu domin kauce wa zaluncin da ake musu."

Ban Ki Moon na neman ɗora Libiya kan Dimokraɗiya

A nasa ɓangaren babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya ce zai jagoranci wani ƙoƙarin ƙasashen duniya na ɗora ƙasar Libya a kan turbar dimokraɗiya, yana mai cewr Majalisar Ɗinkin Duniya a shirye take wajen tallafa wa al'ummar Libya a kan wannan faftuka. Sai dai ya ce ƙoƙarin ginin tubalin dimokradiya ne abu ne da zai ɗauki lokaci.

Sai da kuma wasu mahalarta taron na ganin cewar kamata yayi a bai wa shugaba Ghaddafi damar yin gudun hijira zuwa wasu ƙasashen, musamman ma dai yankin Afrika ko kuma ƙasar Venuzuela, amma kuma wakilan 'yan tawayen ƙasar da suka halarci zauren taron sun soki wannan lamiri. Ministan harkokin wajen ƙasar Spain ya bayyana cewa bai wa Ghaddafi damar yin gudun hijira abu ne da yake halartacce kasancewar kotun hukunta laifukan yaƙi ta duniya ba ta tuhume shi da wani laifi ba kawo yanzu. Shi kuwa ministan harkokin wajen ƙasar Britaniya William Hague yana ganin cewa wajibi ne Ghaddafi ya fuskanci wannan kotu ta ƙasa ƙasa domin ya amsa laifukan yaƙi da keta haƙƙin bil Adama da ya aikata.

Hillary Clinton Libyen Luftangriffe
Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary ClintonHoto: ap

Ita kuwa sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton cewa ta yi yazama lallai a cigaba da yin lugudan wuta a kan shugaba Ghaddafi har sai ya dakatar da harin da yake kai wa farar hula, ta kuma yi kira ga mahalarta taron da su yi magana da murya ɗaya domin kira ga Ghaddafi da ya ajiye mulki ya kama gabansa:

"Dukkan mu ya kamata mu ci gaba da matsin lamba tare da tsangwama ga mulkin Ghaddafi, wannan ya haɗa da ɗaukar matakan ƙarfi da diplomasiyya har sai shi da kansa ya haƙura."

Jamus ka iya ba da gudummawar sake gina Libiya

A nasa ɓangaren ministan harkokin wajen Jamus gido Westrewelle, tayi yayi na taimakawa wajen sake gina ƙasar ta Libya, inda yake cewa:

"Ahalin yanzu dai an shiga wani sabon babi na siyasar Libya kuma wajibi ne a mayar da hankali akan warware rikicin ƙasar a siyasance saboda matakai na soja kawai ba zasu wadatar ba. Wannan shi ne ainihin wannan taron na London, domin nazarin makomar ƙasar ta Libya. Jamus a shirye take wajen tsoma baki a kan wannan manufa. Kazalika a shirye take wajen ba da taimako na jin ƙai domin sake gina ƙasar. Zamu ba da haɗin kai domin cimma wannan manufa".

Ghaddafi na iya hijira zuwa kowace ƙasa ta Afirka

Ana ganin dai matuƙar ya tabbata cewar shugaba Ghaddafi zai yi gudun hijira to kuwa ba zai wuce zuwa ƙasar Venuezula ba saboda abotarsu da shugabga Hugo Chavez na ƙasar, ko kuma ƙasar Zimbabwe ko kuma dai Burkina Faso duba da yadda alaƙar ƙut da ƙut dake akwai tsakanin sa da shugabannin ƙasashen. Har ila yau ana ganin Ghaddafi zai iya tafiya zuwa kowace ƙasa a nahiyar Afrika duba da yadda yake tallafa wa ƙasashen da kuɗin man fetur ɗin ƙasar sa.

Mawallafi: Nasiru Zango
Edita: Ahmad Tijani Lawal