1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon taron gamayyar ƙasa da ƙasa a Doha game da rikicin Libiya

April 13, 2011

Ƙasashen duniya da su ka hallara a birnin Doha sun yanke shawara taimakawa ´yan tawayen Libiya su hamɓarar da shugaba Ƙhaddafi

https://p.dw.com/p/10t6w
Zauren taron Doha game da rikicin LibiyaHoto: picture alliance / dpa

Wakilan ƙasashen yammacin duniya da na larabawa sun kamalla taron da su ka shirya a birnin Doha na ƙasar Qatar domin tunanin hanyoyin taimakawa ´yan tawayen ƙasar Libiya.

`Yan tawaye masu neman kifar da shugaba Mohamar Ƙhaddafi da ƙarfin tuwo sun halarci taron, inda suka yi kira ga ƙasashen Turai su ƙara matsa ƙaimi domin cimma burin da suka sa gaba.

A wani mataki na amsa kira, mahalarta taron sun yanke shawara girka wani asusu na mussamman domin bada tallafi ga yan tawayen Libiya.Sannan a ɗaya wajen, sun buƙaci shugaba Mohamad Khaddafi ya sauka daga karagar mulki.

Ministan harkokin wajen Birtaniya Wiliam Hague ya bayana hujjojin ɗaukar wannan matakai:Ya ce idan ba mu kifar da shugaba Khaddafi ba, to za iya tuhumar gamayara ƙasa da ƙasa da nuna sakaci wajen kare rayukan fararen hula a Libiya

Tsofan ministan harkokin wajen ƙasar Libiya, Musa Kusa da ya juyawa gwamnatin Khaddafi baya, ya kuma samu mafaka a Birtaniya na daga cikin mahalarta taron Doha.

Ita dai Qatar na daga tsirarun ƙasashen larabawa da su ka ɗaurewa ´yan tawayen Libiya gindi, har ma su ka basu tallafin makamai.

Kazalika, fadar mulkin Doha ta bada haɗin kai ga rundunar tsaro ta NATO a yanƙin da ta ƙaddamar a Libiya.

Mawallafi: Yahouza sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman