1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

041011 Syrien UN Resolution

October 5, 2011

Ƙasashen Rasha da China sun hau kujera naƙi game da ƙudurin ɗaukar matakan ladabtar da hukumomin Siriya

https://p.dw.com/p/12m4N
Hoto: picture-alliance/dpa

A yayin da sojojin gwamnatin Siriya ke ci gaba da kai farmaki ga masu zanga-zangar neman sauyi, komitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kasa cimma daidaito kan matakan ladabtar da hukumomin ƙasar.

A wata mahaura da Komitin ya tafka jiya, ƙasashen Rasha da China sun hau kujera naƙi game da ƙudurin da ƙasashen Turai da Amurika suka bukaci a ɗauka kan Siriya.

Bisa dukan alamu dai har yanzu tsugunne ba ta ƙare ba, game da rikicin ƙasar Siriya.A yayin ɓangarorin biyu suka ja daga, ƙasashen duniya sun kasa jituwa game da hanyoyin warware rikicin ƙasar.

Ƙasashe tara daga jimlar ƙasashe 15 na komitin Sulhu suka ƙuri´ar amincewa da ƙuduri, sannan ƙasahe huɗu wanda suka haɗa da Brazil,Afirka da Kudu Indiya da Labanan su ka kaɗa ƙuri´ar 'yan baruwamu, sai Kuma Rasha da China su ka hau kujera naƙi.

Jim kaɗan bayan kamalla mahaura a komitin Sulhu,jikadan ƙasar Siriya a Majalisar Ɗinkin Duniya Walid Muallim,ya godiya ga ƙasashe da su ka ba hukumomin Damscus goyan baya:

"Godiya ta tabbata ga dukan ƙasashe, wanda a cikin wannan mummunan hali da Siriya ta shiga, suke bamu ƙarfin gwiwa da haɗin kai".

Tambayoyin da jama´a da dama ke yi sune shin wane dalilai suka sa Rasha ke nuna goyan baya ido rufe ga ƙasar Siriya ta hanyar yin watsi da matakin da ƙasashen Turai da Amurika ke buƙatar ɗauka ga hukumomin ƙasar.Hilal Khashan wani mai sharhi ne a jami´ar Amurika dake Labanon ya bada haske:

Rasha ta na da murradan da take karewa ne a ƙasar ta Siriya.

Rasha ba za ta amincewa ba ƙasashen yammacin duniya su yi mata sakiyar da babu ruwa, kamar yadda ta faru game da rikicin Libiya.

A yayin da yake bada hujojin kasarsa nan hawa kujera naki jikadan Rasha a komitin Sulhu cewa yayi daukar wannan mataki ba zai taimaka ba a shawo kan matsalar cikin ruwan sanhi.Hanya mafi dacewa injin Vitali Tchourkine itace ce kawai ayi yadda yadda bangarorin biyu masu gaba da juna za su hau tebrin shawara.

Kasar Faransa da ta yi ruwa ta yi tsaki domin daukar matakan hukunta gwamnatin Siriya ta bakin jikadanta Gerard Araud ta bayana matukar bacin rai :

Babu kujerar naki da wata kasa za ta hawa wadda za ta iya wanke hukumomin Siriya da ta´adin da su ka aikata ta hanyar kisan gilla ga al´umarsu.

Itama Susane Rice jikadiyar Amurika a Majalisar Dinkin Duniya cewa ta yi matsayin da kasashen biyu suka dauka abin Allah wadai kuma zai maida hannun agogo baya a yunkurin samar da zaman lafiya a kasar Siriya:Amurika ta ji takaici, ta yadda wannan majalisi ya kasa tabura komai domin ceton Siriya, kuma kuwa zai kara dagula al´amura baki daya.

Saidai duk da wannan komam bayan da aka samu kasashe masu adawa da shugaba Bashard Assad sun yi alkawarin ci gabada gwagwarmaya har sai sun tabbatar da girkuwar demokradiya a kasar Siriya.

Tun dai daga fara rikicin na siyara a watan Maris na wannan shekara zuwa yanzu alkalluma sun ruwaito cewar mutane 2.700 suka rasa rayuka.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Usman Shehu Usman