1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon gasar rubutun littatafai a Frankfurt

Sadissou YahouzaOctober 10, 2010

David Grossman ɗan Isra´ila ya lashe gasar rubutun littatafai ta shekara bana a birnin Frankfurt

https://p.dw.com/p/PacT
David Grossman a bikin baje kolin littatafai na FrankfurtHoto: dapd

Littafin wani marubuci ɗan ƙasar Isra´ila, David Grossman,ya yi nasara zama na ɗaya, daga sahun littatafen da marubuta su ka gabatar, a gasar rubuce-rubucen littatafai da ke wakana ko wace shekara a birnin Frankfurt da ke nan Jamus.

Littafin na David Grossman  ya yi bayyani game da rikici tsakanin Isra´ila da Palestinu da kuma wajibcin cimma masalaha cikin ruwan sanhi.Ya fara ru´buta wannan littafi tun bayan yaƙin shekara 2006 tsakanin Isra´ila da Hizbullahi wanda a ciki ɗansa Uri ya rasa ransa.

Kamar ko wace shekara alƙalai na bayana littafin da ya hi tasiri a gasar bajen kolin littatafai ta birnin Frankfurt, tare da tukuicin Euro 25.000.

Mawalafi:Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmed Tijani Lawal