1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

050812 Griechenland Troika

August 6, 2012

Kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu a ƙoƙarin gwamnatin Girka na fidda ƙasar daga ƙangin talauci

https://p.dw.com/p/15kfA
Newly appointed Greek Prime Minister Antonis Samaras (C) sits between his next Finance Minister Vassilis Rapanos (R) and Foreign Minister Dimitris Avramopoulos (L) during the first cabinet meeting of his government at the parliament in Athens June 21, 2012. Greece's new government promised on Thursday to renegotiate the terms of the country's bailout without endangering its future in the euro, trying to ease social tensions but also risking a showdown with European powers. REUTERS/Yorgos Karahalis (GREECE - Tags: POLITICS BUSINESS)
ƙusoshin gwamnatin GirkaHoto: Reuters

A jiya Lahadi ne tawagar shiyyoyi uku da ta haɗa da ƙurraru daga ƙungiyar Tarayya Turai, Babbar Bankin ƙasashen Turai da Asusun bada Lamuni na duniya, suka kammala tattanawa da gwamnatin ƙasar Girka inda su ka yi bitar halin da ake ciki game da yunƙurin ceto ƙasar daga talaucin da ya mamaye ta.

Ga dukan alamu kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu a ƙoƙarin tsamo Girka daga mumunan halin talaucin da ta shiga.Wannan kalamomi sun hito daga bakin ɗaya daga wakilan Asusun Bada Lamuni na Duniya da ya halarci taron a birnin Athena.Poul Thomsen ya ce gwamnatin ƙasar Girka ta yi abun azo a gani, domin ta fara samun nasara tsarin tsuke bakin aljihu ba tare da fuskantar turjiya daga jam'a ba, kamar abunda ya faru watanin baya.

Baki ɗaya wakilan tawagogin kusuruwowin uku sun yaba da cigaban da aka samu a ka Girka.Ministan taimakon raya ƙasa na Girka Kostis Hatzidadis ya ce za su cigaba da ƙoƙari har sai sun kai ga nasara warware wannan matsala:

"Babban burinmu shine mu tabbatar da dawamar ƙasar Girka cikin rukunin ƙasashe masu amfani da takardar kuɗin Euro, sannan mu kai matsayain da ƙasar za ta tsayawa da ƙafafuwanta.Cilas sai mun ɗauki matakai masu ƙwari domin babban goro sai magogi na ƙwarai.

Euro-Banknoten mit griechischer Euromünze (Foto: DW) // Eingestellt von wa
Hoto: DW

Ya yanzu wannan lokaci mun fara ganin haske cikin al'amarin".

Kasar Girka ta tsara yin tsimi da tanadi da tsabar kuɗi Euro miliyan dubu 11 da rabi a tsukin shekarun 2013 da kuma 2014

A sakamakon tattanawar da suka yi da hukumomin Girka tawagar ƙungiyar tarayya Turai Babbar bankin ƙasashen Turai da Asusun bada Lamuni na duniya, sun haƙiƙance cewar idan dai aka cigaba da haka to ƙasar Girka za ta samun tallafin kuɗin ceto na dalla miliyan dubu 130 da suka alƙawarta mata.Kuma a cikin watan Satumba mai kamawa ake sa ran zuba wani sashe na wannan kuɗaɗe.

Bangarorin da gwamnatin za ta tsimi kuɗin sun haɗa da kuɗaɗen fensho da kuma na tallafi da ake baiwa iyalai masu ɗan ƙaramin ƙarfi.Wannan matakai za su ƙara saka jama'a ƙasa cikin halin uƙuba to amma a cewar Anna Kakava a birnin Athena abinda ya tura kusu wuta ne ya fi wuta zafi.

"Lalle mutane za su ƙara shiga cikin matsalolin rayuwa, to amma idan hakan zai taimaka ƙasar ta kuɓuta daga halin da ta shiga bai zama lefi ba.Ba za a zura ido ba a rungumi ƙaddara ba, cilas sai an ɗauki matakai tsatsaura na kawo ƙarshen wannan masifa".

A yayin da gwamnati da masu goyan bayanta ke tunanin kama hanyar shawo kan matsalolin kuɗin ƙasar, shi kuwa Shugaban gugun jam'iyun adawa Alexis Tsipras,ya dangata mataki da ruɓɓaɓar dubara:

" Ba ni tsammanin tsimin euro miliyan 11 da rabi a shekaru biyu zai tasiri wajen warware rikicin kuɗin Girka, sannan bani tunanin hanyoyin da ake bi a halin yanzu su kai ƙasar ga tundun mun tsira."

An EU and a Greek flag fly in front of ancient Parthenon temple, in Athens, Sunday, June 17, 2012 as Greeks vote in the most crucial elections in decades. Greece voted Sunday amid global fears that victory by parties that have vowed to cancel the country's international bailout agreements and accompanying austerity measures could undermine the European Union's joint currency and pitch the world's major economies into another sharp downturn. (AP Photo/Petros Giannakouris)
Hoto: AP

Wannan rikicin kudi da ya dabaibaiye Girka ya shiga kanun labaru a fagen siyasar Jamus, a wata hira da yayi jiya da jaridar Bild, ministan kuɗin jihar Bavariya Markus Söder ya ce sam, kamata tayi kamin ƙarshen shekara da muke ciki ,Girka ta fita daga sahun ƙasashe masu amfani da Euro, wanda a tunaninsa ita ce hanya mafi dacewa ta kawo ƙarshen matsalar ƙasar.

Mawalladfi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: saleh Umar Saleh