Sahihiyar hanyar warware rikicin Siriya
September 15, 2012Babban mai shiga tsakani a rikicin Siriya Lakhdar Brahimi, ya fadi a wannan Asabar, bayan ganawa tare da shugaba Bashar al-Assad na Siriya cewar tabarbarewar harkokin tsaro a kasar ta Siriya wata barazana ce ga duniya baki daya.
A nashi bangaren, kamfanin dillancin labaran kasar ta Siriya ya ruwaito shugaba Assad na shaidawa mai shiga tsakanin cewar, nasarar aikin daya ke gudanarwa ta dogara ne ga manyan kasashen da ke samar da makamai ga 'yan tawayen Siriya, tare da basu horo da kuma samar musu da kudaden gudanar da ayyukan su, inda yayi kira a gareshi daya nemi su dakatar da yin hakan.
Kalaman na shugaba Assad dai na zuwa ne bayan da Fafaroma Benidikt na 16 da ke fara ziyarar aiki a kasar Lebanon wadda ke makwabtaka da Siriyar ya kwatanta shigo da makaman da ake yi zuwa Siriya a matsayin babban zunubi, tare da yin kira ga dakatar da hakan.
Ita kuwa kungiyar kare hakkin jama'a ta kasar Siriya, wadda cibiyar ta ke birnin London na Birtaniya cewa ta yi kimanin mutane 160 ne suka mutu a wannan Jumma'ar kadai, sanadiyyar bata-kashin da aka yi a kasar ta Siriya.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman