Sahel: Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan tallafi
October 19, 2020Talla
Shugaban hukumar samar da agaji ta MDD, Mark Lowcock, ya ce dala biliyan guda da kasashen Denmark da Jamus da Tarayyar Turai da ma ita kanta Majalisar Dinkin Duniyar za su samar na da amfani matuka, amma kasashen na fama da rashin gwamnatoci na gari.
Kasashen na yankin Sahel da ake batu a kan su dai su ne Burkina Faso da Mali da kuma jamhuriyar Nijar.
Haka nan baya ga batun rashin gwamnatoci a kasashen, Majalisar Dinkin Duniyar ta ce akwai matsalar yawan haihuwa babu tanadi da kuma sauyin yanayi.