Sabuwar gwamnatin Masar
August 1, 2012Talla
Fiye da wata guda bayan rantsar da Mohammad Mursi a matsayin shugaban ƙasar Masar, a yau Laraba Firaministan da ya naɗa Hisham Kandil, ya baiyana sunayen majalisar ministocin ƙasar.
Daga jerin ministocin gwamnatin dake barin gado, ƙalilan suka yi nasara yin tazarce.
Ministocin da suka samu nasara ci gaba da aiki, sun haɗa da Ministan kuɗi Momtaz al-Said, da kuma ministan harakokin waje Mohammad Kamel.
A lokacin da shugaba Mohammad Mursi ya naɗa Firaminista a watan da ya gabata,ya umurce shi ya fi bada fifiko ga ƙurewa a wurin zaɓen ministoci, ba tare da la'akari da ɓangarancin siyasa, addini ko na ƙabila ba.
Mawallafi:Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu