1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Firaiministan Isra'ila na ziyara a Masar

Ramatu Garba Baba
March 21, 2022

Firaiministan Isra'ila Naftali Bennett ya kai wata ziyarar ba-zata Masar inda kasashen biyu ke fatan bude sabon babi a inganta huldar diflomasiyya.

https://p.dw.com/p/48ocA
Ägypten Scharm el Scheich | Treffen Ministerpräsident Israel Bennett und Präsident al-Sisi
Hoto: EGYPTIAN PRESIDENCY/AFP

Firaiminista Bennet ya baiyana fatan ganin samun hadin kan Shugaba Abdel Fattah al-Sisi don karfafa dangantaka da kuma hada kai a samar da tsaron yankunan biyu kamar yadda aka amince a wata yarjejeniya da kasashen suka cimma tun a shekarar 1979. Baya ga haka, Isra'ila da Masar suna son ganin sun fadada harkar sufuri ta yadda kai tsaye za su iya shiga kasashen juna.

Hakazalika rahotanni sun tabbatar da isar Yarima Mohammed bin Zayed al-Nahyan na Abu Dhabi a Masar inda ake sa ran za su gana da Shugaba al-Sisi a wani katafaren wurin shakatawa da ke Sharm El-Sheikh. Babu dai bayani kan dangantakar haduwar shugabanin a lokaci guda.Ziyarar ta kasance irinta ta farko da wani babban jami'in Isra'ila ke kai wa kasar Masar.