1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar cuta ta bulla a China

January 18, 2020

Hukumomi a Amirka, sun shirya bincike na musamman kan fasinjojin da ke shiga kasar ta wasu filayen jirage uku, a kokarin kauce wa wata cutar da ta bulla a China.

https://p.dw.com/p/3WOcO
China Wuhan Krankenhaus
Hoto: Getty Images/AFP/N. Celis

Amirka ta shirya binciken ne a kokarin maganta yaduwar cutar wadda ya zuwa yanzu ta kashe mutane biyu wasu da dama kuwa ke fama da ita a China.

Cutar dai ta dauki hankalin kasashen duniya, koda yake har yanzu ba kai ga tantance ta ba.

Cibiyar da ke yaki da cututtuka ta Amirkar, ta ce gwajin yanayin zafin jikin masu shiga kasar ne tare da neman sanin wasu alamun matsalolin lafiya da suke ji suke yi.

Cutar ta kuma bulla ne a wani birnin da ake kira Wuhan a kasar ta China.

Kimanin mutum dubu biyar ne za a a bincike su daga cikin wadanda ake sa ran za su shiga Amirkar daga yankin da matsalar ta bulla a kasar ta China.