1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jama'a na kauracewa rijistan a Côte d'Ivoire

Julien Adayé GAT
June 12, 2020

A wani mataki na shirye-shiryen zaben shugaban kasa na watan Oktoba mai zuwa a kasar Côte d'Ivoire, Hukumar zaben kasar ta kaddamar da aikin sabinta rijistar masu zabe.

https://p.dw.com/p/3dhCQ
Elfenbeinküste Wahl 2018 |
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A ranar Litinin da ta gabata ce hukumar zaben kasar ta Côte d'Ivoire wato CENI ta koma aikin sabinta rijistar masu zaben da kuma rijistan sunayen matasan da suka cika shekarun zabe a yanzu a cikin sabon girgam din zaben. Za a dai share makonni biyu ana gudanar da wannan aiki. Sai dai kuma duk da kiraye-kirayen da jam'iyyun siyasa suka yi ga jama'a na su fito su yi rijistar, da dama ba su fito ba inda cibiyoyin rijistar suka kasance kusan kango. Shugaban hukumar zaben kasar ta Côte d'Ivoire Kuibiert-Coulibaly Ibrahim ya yi karin bayani kan wannan aiki da suka soma: '' Muna jiran duk dan kasar Côte d'Ivoire da ya cika sharuddan da ake bukata domin yin rijistarsa a girgam din zaben. Muna sa ran rijistar mutane kimanin miliyan hudu da rabi zuwa miliyan biyar a sabuwar rijistar"

Gardama tsakanin 'yan siyasar na adawa da masu mulki a game da karuwar adadin masu kada kuri'ar

Umstrittenes Verfassungsreferendum in der Elfenbeinküste
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

A cibiyar rijistar sabbin masu zabe ta unguwar Yopougon ta arewacin birnin Abidjan ana samun 'yan kwarorin mutane da ke zuwa yin rijistar. Nadege Soumahoro na daga cikin wadanda suka yi rijistar ya kuma bayyana farin cikinsa yana mai cewa: "Na yi farin ciki sosai domin yau na kai shekarun balaga, wanda ya ba ni 'yancin yin zabe. Na yi murna da yin rijistar da za ta ba ni damar zaben wanda nake ra'ayi." Aikin rijistar sabbin masu zabe na gudana ne tare da na yi wa girgam din zaben gyara huska wanda ake sa ran zai kunshi mutane kimanin miliyan 11 wato kusan ninki biyu na yawan wadanda girgam din zaben na yanzu ya kunsa. Eric Tohou na jam'iyyar Liber ya bayyana dalillan da suka sanya adadin masu zaben zai karu: "Yawan al'ummar kasar nan ya karu sosai a shekaru 10 na baya bayan nan, kuma ba a gudanar da aikin kidayar al'umma a tsukin shekarun ba. Dan haka muke sa ran a yanzu adadin mutanen da suka cancanci kada kuri'ar zai kai mutun miliyan 10 zuwa 12. Sai dai wasu 'yan siyasar kasar na ganin adadin mutanen da ake hasashen sun karu a tsukin shekarun 10 bai kai wanda wasu ke fada ba. Mariuzs Konan dan majalisar dokoki daga jam'iyyar PDCI na daga cikin masu irin wannan ra'ayi: ''A cikin shekaru 10 na bayan nan adadin mutanen da suka karu a girgam din zaben bai wuce miliyan daya da rabi ba. Dan haka ba wanda a yau zai zo ya ce mana za a iya rijistar mutane miliyan hudu da rabi zuwa miliyan biyar a cikin makonni biyu kacal. Ba zan taba amincewa da wannan ba."

.