1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunƙurin warware rikicin Siriya

June 30, 2012

Kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da sabbin matakan shawo kan rikicin Siriya.

https://p.dw.com/p/15Oly
The United Nations Security Council meets at the United Nations in New York to discuss the ongoing violence in Syria April 21, 2012. The U.N. Security Council unanimously adopted a resolution on Saturday that authorizes an initial deployment of up to 300 unarmed military observers to Syria for three months to monitor a fragile week-old ceasefire in a 13-month old conflict. REUTERS/Allison Joyce (UNITED STATES - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Rahotanni daga Jeniva na ƙasar Switzerland na cewar an cimma daidaito tsakanin wakilan ƙasashe na kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya dake gudanar da taro akan Siriya.

Ƙasashen, waɗanda ke ƙoƙarin tsara wani shiri na gwamnatin haɗin kan ƙasa ta wucin gadi a Siriya, babban mai shiga tsakani a rikin ƙasar, Kofi Annan ne ya gabatar da shawarar haka.

Tunda farko sun yi ta gamuwa da tarnaki daga ƙasashen China da Rasha waɗanda basu yarda da saukar shugaba Bashar al-Assad daga mulkin ba.

A cikin sanarwar da ya bayyana a gaban waklilan, manzon musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya ya sanar da cewar gwamnatin wucin gadin za ta ƙunshi wakilan gwamnatin Siriya dake ci yanzu kafin a kai ga shirya wani zaɓe:

" Ya ce a cikin irin wannan hali ya zama wajibi shugabannin sun ɗauki matakan da za su gyara gobe domin kawo sauyi

kuma ina fatan gwamnatin Bashar al-Assad za ta bada haɗin kai wajen ƙaddamar da wannan shiri."

A ƙarƙashin wannan shiri dai shugaba Assad zai ci gaba da riƙe matsayin shugaban ƙasa na je ka- na-yi ka.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

 Edita :    Saleh Umar Saleh