1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunkurin warware rikicin Siriya

January 31, 2013

Amirka da Rasha za su gana da 'yan adawar Siriya domin samun mafita ga rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/17W66
U.S. Secretary of State Hillary Clinton (R) and Russian Foreign Minister Sergei Lavrov pose for photographers during the 48th Munich Security Conference at the Bayerischer Hof hotel in Munich, February 4, 2012. The Security Conference is a three-day event bringing together top defence and diplomacy officials from around the world discussing the winding down of the NATO engagement in Afghanistan and other looming challenges. REUTERS/Jim Watson/Pool (GERMANY - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Wata sanarwar da fadar shugaban Amirka ta White House ta fitar a wannan Alhamis (31.01.13), ta nunar da cewar mataimakin shugaban na Amirka Joe Biden zai tattauna hanyar kawo karshen rikicin Siriya tare da ministan kula da harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da kuma jagorar 'yan adawar kasar ta Siriya Moaz al-Khatib a wannan Asabar. Biden, zai yi wannan ganawar ce a gefen babban taron da zai mayar da hankali akan lamuran tsaro a birnin Munich na nan Jamus, wanda kuma zai bashi damar tattaunawa tare da shugabannin Jamus da Faransa da kuma Birtaniya.

Taron dai na zuwa ne bayan da wasu rahotannin da ba'a tabbatar da su ba na nuna cewar Isra'ila ta kaddamar da hari akan wata cibiyar biciken makamai ta soji da kuma wani jerin gwanon motocin da ke dauke da makamai akan iyakar Siriya da Lebanon.

A dai wannan alhamis ne gwamnatin kasar ta Amirka ta yi gargadi game da yiwuwar gwamnatin Siriya ta mikawa mayakan kungiyar Hizbullahi da ke kasar Lebanon, wasu daga cikin makaman da ta mallaka.

A can baya dai Amirka ta yi Allah wadai da rasha game da hawan kujerar na ki ga wasu kudurorin Majalisar Dinkin Duniya akan Siriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou