Sabon yunƙurin warware rikicin Siriya
June 30, 2012Rahotanni daga Jeniva na ƙasar Switzerland na cewar an cimma daidaito tsakanin wakilan ƙasashe na kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya dake gudanar da taro akan Siriya.
Ƙasashen, waɗanda ke ƙoƙarin tsara wani shiri na gwamnatin haɗin kan ƙasa ta wucin gadi a Siriya, babban mai shiga tsakani a rikin ƙasar, Kofi Annan ne ya gabatar da shawarar haka.
Tunda farko sun yi ta gamuwa da tarnaki daga ƙasashen China da Rasha waɗanda basu yarda da saukar shugaba Bashar al-Assad daga mulkin ba.
A cikin sanarwar da ya bayyana a gaban waklilan, manzon musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya ya sanar da cewar gwamnatin wucin gadin za ta ƙunshi wakilan gwamnatin Siriya dake ci yanzu kafin a kai ga shirya wani zaɓe:
" Ya ce a cikin irin wannan hali ya zama wajibi shugabannin sun ɗauki matakan da za su gyara gobe domin kawo sauyi
kuma ina fatan gwamnatin Bashar al-Assad za ta bada haɗin kai wajen ƙaddamar da wannan shiri."
A ƙarƙashin wannan shiri dai shugaba Assad zai ci gaba da riƙe matsayin shugaban ƙasa na je ka- na-yi ka.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh