1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici ya sake barkewa a kasar Sudan

Binta Aliyu Zurmi MAB
June 12, 2023

Bangarorin da ke rikici da juna sun saka komawa gidan jiya, jim kadan bayan cikar wa'adin tsagaita wuta ta sa'o'i 24 da aka cimma, wacce ta taimaka wajen kai dauki ga mabukata.

https://p.dw.com/p/4SSLp
Rashin kwanciyar hankali a kazanta a Khartum babban birnin SudanHoto: AP

Tun a jranar lahadi ne aka fara jin karar fashe-fashe a birnin Khartoum, wanda mazauna garin suka ce shi ne irin shi mafi muni a baya-bayan nan.A Ondurman ma, rahotannin sun tabbatar da ci gaba da ruwan makamai irin na atilare. A baya, an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke gaba da juna, sai dai ba ta yi wani tasiri ba.

Amirka da Saudiyya da suka taimaka aka cimma yarjejeniyar a baya sun ce wannan tsagaita wuta an sami damar kai wa mabukata daukin gagawa. Rikicin da ya samo asali a kan neman shugabanci na ci gaba da lakume rayukan mutane tatre ma da raba dubbai da matsugunnansu.