1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici ya barke a Sudan ta Kudu

Ahmed Salisu
May 21, 2020

Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewar mutane da dama sun rasa rayukansu a wani sabon rikici da ya barke a wasu yankunan kasar kuma baya ga asarar rai an samu asarar dukiya.

https://p.dw.com/p/3cam2
Äthiopien Addis Abeba Salva Kiir Mayardit und  Hailemariam Desalegn
Hoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

Wata sanarwa da kungiyar nan ta Red Cross ta fidda wadda ta tabbatar da wannan labari, ta ce daga cikin wadanda suka mutu a inda rikicin ya wakana a jiya Laraba a jihar nan ta Jonglei har da wasu ma'aikatan jinya guda biyu da ke aiki da kungiyar nan ta Doctors Without Borders.

Sanarwar ta Red Cross dokokin da aka sanya na takaita zirga-zirga saboda annobar coronavirus sun taimaka wajen gaza kaiwa ga wajen da aka yi rikicin domin shawo kansa da kuma kwashe wanda suka jikkata don kaisu asibiti da nufin yi musu magani.

Tuni dai jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke aiki a Sudan ta Kudu din suka sanar da isar wata tawaga arewacin jihar Jonglei domin gudanar da bincike kan musababbin tashin rikicin.