1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Ta'azzarar nau'in Delta a Turai da Asiya

Zainab Mohammed Abubakar
July 22, 2021

A yayin da nahiyoyin Turai da Asiya ke fafutukar yaki da bazuwar sabon nau'in cutar corona mai suna Delta, sama da rabin al'ummar Turai ne aka yi wa allurar riga kafin Covid-19.

https://p.dw.com/p/3xtXF
Deutschland Hochwasser Katastrophe Ahrweiler Coronavirus Impfbus
Hoto: Christian Mang/REUTERS

Babban bankin Turai ya sanar da cewar, rashin sanin tabbas game da yaduwar nau'in na Delta, na nufin barin hanyoyin fitar da kudi bude, domin tabbatar da cewar kokarin farfado da tattalin arziki bai fuskanci wani tarnaki ba.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da cewar, ana samun karuwar masu kamuwa da sabon nau'in wannan cuta da ta zama ruwan dare a fadin duniya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin bude wasannin guje guje da tsalle tsalle na Olympics da aka jinkirta gudanarwa da shekara guda a birnin Tokyon kasar Japan a gobe Juma'a. Wasannin da za a gudanar ba tare da 'yan kallo ba, daura da tsananta dokokin yaki da corona.