1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon kundin tsarin mulki a Somaliya

Usman ShehuAugust 2, 2012

Bisa ga dukkan alamu kasar Somaliya ta kama hanyar dawo da doka a kasar, inda yanzu aka samu sobon kundin tsarin mulki

https://p.dw.com/p/15ia0
In this photo of Wednesday July 25, 2012, Somalia's constituency assembly members hold up copies of the proposed new constitution during the beginning of a nine-day meeting on Wednesday to examine, debate and vote on the proposed new constitution, in Mogadishu, Somalia. Somali leaders are debating a new constitution that protects the right to abortion to save the life of the mother and bans the circumcision of girls. (Foto:Farah Abdi Warsameh/AP/dapd)
Matan da suka hallarci zauren rubuta kundin tsarin mulki a SomaliyaHoto: dapd

Sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya taya ƙasar Somaliya murnar samun sabon kundin tsarin mulki. Wannan ya zo sa'o'i kaɗan bayan amincewa da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar da wakilan ƙabilu 800 su ka yi. Bisa sabon tsarin mulkin mata suna da ta ce wa, ciki harda iya zubar da ciki idan rayuwar mace ta shiga haɗari.

Ƙasar ta Somaliya ta shafe fiye da shekaru 20 bata da cikakkiyar gwamnatin tsakiya. Kazila wa'adin dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD zai kawo ƙarshe cikin watan Agusta, yayin da ake saran a wannan lokaci, ƙasar za ta samu sabuwar majalisar dokoki da sabon Shugaban ƙasa.

Mawallafi: Suleiman Babayo

Edita: Usman Shehu Usman