1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon kamun da jam'iyyar APC ta yi a Sokoto

December 9, 2013

Gwamnan jihar Sokoto ya ba da sanarwar shiga cikin jam'iyyar APC tare da dukkan Muƙarrabansa.

https://p.dw.com/p/1AVmA
Wahlen Nigeria Genral Muhammadu Buhari
Hoto: AP

A wani taro na masu ruwa da tsaki na gwamnatin jihar Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya, a yammacin wannan Litinin (09. 12. 13) ne bayan kammala taro na majalisar zartar wa ta jihar, da kuma shugabannin ƙananan hukumomi 23 na Jihar, sun bayyana canza sheƙa zuwa jam'iyyar adawa ta APC dukkaninsu. Taron dai ya samu halartar gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko da mataimakinsa Mukhtar Shehu Shagari.

Wakilinmu na Sokoto, Aminu Abdullahi Abubakar ya shaida mana cewar, taron ya bayyana fice wa daga jam'iyar PDP zuwa APC daga wannan Litinin kuma tuni aka sauya launin fenti na ofishin PDP zuwa fari, wanda ke muna alamun kowane lokaci za a iya yin na jam'iyar PDP. Gwama Aliyu Magatakarda Wamakko dai na cikin gwamnonin biyar da suka fice daga PDP zuwa APC kuma hakan ya tabbata ne bayan da a wannan Lahadin (08.12.13), gwamnan ya halarci wani taro da wasu gwamnoni na PDP suka yi da shugaban ƙasa Dokta Goodluck Ebele Jonathan. Sai dai kuma wakilin na mu ya ƙara da cewar, wata majiyar da ba a tantace ba, ta ce mataimakin gwamnan jihar ta Sokoto, Mukhtari Shehu Shagari ba zai bar jam'iyyar PDP ba wato yana cikinta har ya zuwa yanzu.

Mawallafi : Aminu Abdullahi Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh