1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon iftila'in girgizar kasa a Turkiyya

February 20, 2023

Rahotanni daga kan iyakar kasashen Turkiya da kuma Siriya sun yi nuni da cewa an samu aukuwar girgizar kasa da yammacin Litinin din nan mai karfin maki 6.4.

https://p.dw.com/p/4Nlcp
Syrien Aleppo | Zerstörte Gebäude nach Erdbeben
Hoto: Muhammed Said/AA/picture alliance

Sabuwar girgizar kasar na zuwa ne makwanni biyu bayan da kasashen biyu suka fuskanci mummunan girgirzar kasar da ta yi sanadiyar rayukan dubban mutane.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa girgizar kasar ta wannan litinin din ta lalata gine-gine a yankin Antakya wanda shi ma ya fuskaci girgizar kasar ta makwanni biyu da suka gabata. Wata mazauniyar yankin mai suna Muna Omar, da ke cikin tantin da suke samun mafaka a yanzu ta ce ta shiga cikin tashin hankali domin yadda ta ji kasa tamkar zata rabe gida biyu.