1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnan Kano ya fara rusau

June 3, 2023

Sabuwar gwamnatin Kano ta umurci hukumomin da ke karkashinta su tabbatar sun rusa gine-ginen da aka yi a filayen masallatai da makabartu da asibitoci da wurin shakatawar yara da kuma kasuwanni.

https://p.dw.com/p/4S9nZ
Sabon gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir YusufHoto: Kyusufabba/Twitter

Sabon gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya Abba Kabir Yusuf ya fara rusa gine-ginen da ya zargi tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar da su ba bisa ka'ida ba.

Wakilin DW a Kano Nasir Salisu Zango ya ce tun a ranar Juma'a da daddare gwamnan da kanshi ya jagoranci rusa wani katafaren gini da ke jikin Filin Sukuwa a unguwar Nasarawa GRA.

Kawo safiyar Asabar din nan, jama'an gari sun garzaya inda aka yi rusau din, inda wani faifan bidiyo ke nuna yadda suke jidar kayan gine-gine irinsu rodi da kofofi da sauran kayayyaki.