1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sabon gidan adana kayan tarihin Damagaram

Lawan Boukar RGB
March 22, 2022

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta sanar da bude wani sabon gidan kayayyakin tarihi irinsa na farko a jahar Damagaram domin masu yawon bude ido. 

https://p.dw.com/p/48r2C
Palast des Emirs von Damagaram in Zinder, Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Wakillan Asusun raya kasashe masu tasowa na kasar Jamus (GIZ) da kuma Dokta Awagana Elhaj Ari daga jami'ar Leipzig ta kasar Jamus ne suka ziyarci dakin karanta litattafan tarihi masu rubutun ajami gami da kanori ga hukumomin Damagaram, gwamnatin Jihar ce ta bude gidan kayan tarihin irinsa na farko a hukumance domin amfanin al'umma da kuma masu yawon bude ido. 

Shi dai wannan aikin gina dakunan karanta litattafan da adanon kayan tarihi da aka ma sunan gidan litattafan tarihi Shatima da ma’aikatar ministan harkokin wajen kasar Jamus tare da tallafin Asusun raya kasashe masu tasowa na kasar Jamus da cewar GIZ suka saka ta hanyar jami'ar Leipzig da ke a kasar ta Jamus, ya dai lakume zunzurutun kudaden sefa da suka haura miliyan goma sha uku.

A yayin da yake jawabin kaddamar da bude gidan tarihin a hukumance, magatakardan gwamnan Jihar Damagaram Maman Harou,   godiya yayi ga kasar ta Jamus. A yanzu haka dai jama’a na ci gaba da yin tururuwar ta hanyar kai ziyara gidan domin ganin abin da ke boye da ya fito a fili.