1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Firaministan da soji suka nada ya je kasar Chadi

August 16, 2023

Sabon firaministan na Nijar ya ce ziyara ce ta nuna 'yan uwantaka a tsakanin sojojin Nijar da suka kwace iko daga hannun farar hula da kasar Chadi tare da nuna 'yancin Nijar na zama kasa mai cin gashin kanta.

https://p.dw.com/p/4VDgP
Hoto: Presidency of the Republic of Chad/AA/picture alliance

Firaministan Jamhuriyar Nijar da sojoji suka nada Ali Mahaman Lamine Zeine ya kai ziyara kasar Chadi a ranar Talatar da ta gabata, inda ya gana da shugaban gwamnatin mulkin soji ta kasar ta Chadi, Mahamat Idriss Déby.

Mahukunta a birnin N'Djamena suka ce ziyarar aiki ce sabon firaministan ya kawo musu, yayin da a nashi bangaren Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce ya je kasar ta Chadi da zummar isar da sakon fatan alheri daga shugaban gwamnatin mulkin soji ta Nijar. Lamine Zeine ya ce sun tattauna da hukumomin Chadi a kan hanyoyin da za a bi wajen bude hanyar tattauna rikicin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin da ya faru da kuma nuna cewa Nijar kasa ce mai cikakken 'yanci.

Ziyarar na zuwa ne yayin da shugabannin rundunonin sojojin kasashen yammacin Afirka suka ce sun shirya gudanar da taro a birnin Accra na Ghana a ranar Alhamis, domin nufin tattauna yiwuwar kutsawa da makami Nijar don mayar da shugaba Mohamed Bazoum a kan kujerar mulki.