Sabon babin dangatakar EU da kasar Burma
January 6, 2012A matsayin martaninta ga gyare-gyaren siyasa da ke wakana a kasar Burma Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta bude ofishinta a Rangoon babban birnin wannan kasa. Kakakin Catherine Ashton, kantomar kungiyar kan manufofin ketare ya ce ofishin zai rinka gudanar da ayyukan taimako a baya ga taka rawa a fannin siyasa. To amma kakakin ya ce ofishin ba shi da wakilici a hukumance. Bayan ganawarsa da shugaban adawar kasar, Aung San Suu Kyi a birnin Rangoon minstan harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya ce an fara ganin sauyin da ke wakana a gwamnatin mulkin sojin kasar ta Burma a kasa.To ama kuma ana bukatar yin matsin lamba ga gwamnatin farar hula da ke mulkin kasar. Hakazalika yayin ganawarsa da Shugaban Sein Thein, Hague ya sake yin kira da asaki dukkan firsinonin siyasa. A hukumance dai ita gwamnatin da aka girka a kasar ta Burma a watan Maris bara gwamnati ce ta farar da har yanzu ake damawa da tsoffin janar janar na soji da magoya bayan gwamnatin mulkin soji da dama a cikinta.
Mawalllafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu