Sabon babi ga kasar Masar
Misrawa sun yi ta kwarara zuwa Dandalin Tahrir don bikin hambarar da Shugaba Mohammed Morsi. A ranar Laraba da dare sojoji suka sanar cewa za su dora gwamnatin farar hula ta wucin gadi kafin a shirya sabbin zabuka.
Sabon shugaban riko
An ratsar da shugaban kotun kolin kundin tsarin mulkin Masar, Adli Mansour a matsayin shugaban rikon kasar bayan da Misrawa suka wayi gari ranar Alhamis cikin wani sabon yanayin siyasa. Bayan kwanaki ana bore da tashe-tashen hankula, rundunar sojojin Masar ta hambarar da Shugaba Mohammed Morsi a ranar Laraba da yamma.
'Nesa da siyasa'
Ministan tsaron Masar kuma hafsan hafsoshin soja Janar Abdel Fattah al-Sisi ya sanar ta gidan telebijin kasar cewa an cire Morsi daga kan mukamin shugabancin kasa. Bai yi karin bayani game da tsawon lokacin gwamnatin riko ba, amma ya jaddada cewa dakarun sojoji za su ci gaba da zama "nesa da siyasa".
Kwanciyar hankali da lumana
An samu kwanciyar hankali a birnin Alkahira kwana guda bayan an hambarar da Morsi, sai dai sojoji sun kasance a ko'ina cikin birnin don hana tabarbarewar halin da ake ciki.
Masar a cikin shagulgula
An yi ta bukukuwa tare da wasan wuta kamar nan a birnin Alkahira bayan da sojoji suka ba da sanarwar hambarar da shugaban kasa a ranar Laraba da yamma. Miliyoyin masu adawa da Morsi a biranen dake fadin kasar sun nuna farin cikinsu.
Murna matuka
Bayan kwanaki ana gudanar da manyan zanga-zangogi, masu adawa da Morsi sun ji dadin matakin da sojoji suka dauka. Duk da cewa an zabe shi ne ta hanyar demokradiyya, amma da yawa daga cikin 'yan kasar ba su amince da gwamnatin Morsi ba, suna masu zarginsa da raba kan 'yan kasa tare da jefa Misrawa cikin kuncin rayuwa.
Matasa 'yan juyin juya hali
Lokacin da sojoji suka ba wa Morsi wa'adi da ya warware rikici tsakaninsa da 'yan adawa, sun gindaya sharadin cewa idan hakan bai faru ba, to za su sanya ido kan aiwatar da wani tsari da zai kunshi dukkan bangarori da jam'iyun siyasa, ciki har da matasa wadanda suka fara wannan "gagarumin juyin juya hali."
Magoya bayan Morsi sun bijire
'Ya'yan Kungiyar 'Yan uwa Musulmi da sauran magoya bayan Morsi da suka taru a harabar masallacin Raba El-Adwyia dake tsakiyar birnin Alkahira, sun rike hotunansa yayin da ake karanta sanarwar rundunar sojojin Masar ta gidan telebijin kasar.
"Cikakken juyin mulki"
Morsi yayi tir da sanawar sojojin da cewa wani "cikakken juyin mulki ne." A cikin wata sanarwa da aka watsa ta shafin Twitter na ofishin tsohon shugaban na Masar, an rawaito Morsi na cewa matakan da sojojin suka dauka daidai suke da "cikakken juyin mulki wanda dukkan al'ummar kasa masu son 'yanci da walwala suka yi watsi da shi."
Sabbin zabuka
Rundunar sojojin wadda ba a fayyace rawar da za ta taka tun bayan juyin juya halin kasashen Larabawa ba, ta sanar da wata "taswirar hanya da za ta karfafa al'ummar Masar." Janar Abdel Fattah al-Sisi ya ce za a kafa wata gwamnatin 'yan takarda kafin a shirya zabuka.