1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin takunkumai ga China da Rasha

March 10, 2021

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya ce Jamus na fatan kyakkyawar alakarta da Amirka za ta share fage na sanya takunkumin hadin gwiwa kan kasashen China da Rasha.

https://p.dw.com/p/3qQ56
New York | UN-Sicherheitsrat zu Krieg in Syrien | Heiko Mass, deutscher Außenminister
Hoto: Getty Images/AFP/T.A. Clary

Maas ya ce akwai bukatar abokan huldar su yi aiki tare don kare bukatunsu a yanzu da kasashen ke da karin fahimtar juna ba kamar yadda yake a lokacin mulkin tsohon shugaba Donald Trump ba.

Jamus dai ta sanya takunkumi kan Rasha tare sauran kawayenta na kungiyar EU kan yadda Fadar Kremlin ke bai wa 'yan awaren Ukraine makamai da kai hari kan masu adawa da shugana Vladimir Putin.