1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin shugabannin Masar bisa tafarki na dimokraɗiya

January 18, 2012

Jam'iyyar 'yan uwa musulmi da ta Salafiya sune manyan waɗanda suka yi nassara a zaɓen ƙasar Masar. Wannan nassara ta su ta tabbata ne a zaɓen majalisun dokokin da aka gudanar cikin 'yanci da walwala

https://p.dw.com/p/13lOB
Senior members of Egypt's Muslim brotherhood Saad el-Katatni, right, Mohamed Morsi centre, and Essam el-Erian hold a press conference in Cairo, Egypt, Wednesday, Feb. 9, 2011. Arabic sign reads " The Muslim Brotherhood, press conference on the latest situation in Egypt". (AP Photo/ Mohammed Abou Zaid)
Shugabannin Jam'iyyar 'yan uwa Musulmi a MasarHoto: AP

A karon farko cikin shekaru da dama al'umar Masar sun kaɗa ƙuri'a cikin 'yanci da walwala. Sun kuma zaɓi Jam'iyyar Islama domin ta jagorance su. Ko da yake sai a ƙarshen wannan watan na Janairu ne ake sa ran samun cikakken sakamakon zaɓen majalisun dokokin da aka gudanar, amma a baiyane ta ke cewa Jam'iyyar 'yan uwa musulmi wato Muslim Brotherhood za ta sami kashi 46 cikin ɗari na kujeru 498 a majalisar dokokin.

Bayan jam'iyyar Muslim Brothers dake murnar samun nasara a zaɓen ita ma jam'iyar Salafiya mai matsanancin ra'ayi wadda ke biye a matsayin ta biyu ta na farin cikin samun kashi 25 cikin ɗari na kujerun majalisar dokokin duk da cewa sabuwa ce a fagen siyasar ƙasar ta Masar. Jam'iyyar wadda ke nufin haske kamar yadda ta kira kanta bata wuce watanni shida da kafuwa ba.

A wannan zaɓe dai akwai jiga-jigan 'yan siyasa kamar Amr Moussa tsohon shugaban ƙungiyar ƙasashen larabawa wanda mai yiwuwa ake fatan zai tsaya takarar shugabancin ƙasar, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa akan yadda dimokraɗiyyar ke gudana da kuma ya yi ammana da sakamakon zaɓen.

Muslim Brotherhood students hold a copy of the Quran during a protest at the al-Azhar university in Cairo, Egypt, Wednesday, April 16, 2008. Thousands of Muslim Brotherhood students in two Egyptian universities demonstrated Wednesday against the jailing of 25 members of the group for membership of an outlawed organization and anti-government activities. (AP Photo/Hossam Ali)
Magoya bayan jam'iyyar 'yan uwa Musulmi a lokacin wata zanga zanga a birnin AlkahiraHoto: AP

Jam'iyyun masu gwagwarmayar neman 'yanci na dandalin Tahrir basu taka rawar a zo a gani ba, haka ma dai magoya bayan tsohuwar gwamnatin Mubarak waɗanda suka sami kujeru 20 a majalisar dokokin.

Jam'iyyar 'yan uwa Muslim da takwarata ta Salafiya suna ganin nasarar da suka samu a matsayin riba ce suka girba ta gwagwarmayar tafarkin addini da suka daɗe suna aiwatarwa tsawon shekaru da dama, musamman ayyukansu na alheri da jajircewa da suka zama babban ƙalubale ga tsohuwar gwamnatin Mubarak. Baya ga salon yaƙin neman zaɓe Jam'iyyar Muslim Brotherhood ita ce jam'iyyar da ta fi tsari da kamala, wadda ma tun gabanin wa'adi ta tsara jadawalin majalisar gudanarwar gwamnatin da za ta kafa.

Kasancewar Jam'iyar ta Muslim Brotherhood ba ta sami gagarumar rinjayen da za ta iya kafa gwamnati ita kaɗai ba, ya zama wajibi ta nemi abokiyar ƙulla ƙawance. Musamman dai babu Jam'iyyar da za ta iya ɗaukar ragamar mawuyacin halin da Masar ɗin ke ciki ita kaɗai a cewar wani ɗan jarida a birnin Alkahira El-Gawhary, wanda yace baya tsammanin Jam'iyyar 'yan uwa Muslmi wadda ke da sassaucin ra'ayi za ta yi haɗin gwiwa da Jam'iyyar Salafiya. Yana mai cewa jam'iyyun biyu suna da saɓanin ra'ayi akan yadda za'a tafiyar da siyasa a muslunci.

Ägypten Wahlen Moslembruderschaft Beteiligung Symbolbild Bildmontage aus dem Logo der Muslimbrüder in Ägypten und einer Wahlurne mit ägyptischer Flagge. Grafik DW/FLorian Meyer
Tambarin Jam'iyyar 'yan uwa Musulmi ta ƙasar MasarHoto: DW

" Ina ganin ya danganta ne ga aƙida. Jam'iyyar 'yan uwa musulmi jam'iyya ce da ta rungumi kowa kuma ta ke da ƙima da martaba to amma wasu masu tsananin kishin islama na ɗaukar ta a matsayin wadda ta tsinci dami a kala. Tsawon watanni ta na tattauna yadda za ta aiwatar da salon mulki irin na Turkiya to amma kada a manta damar da suke da ita taƙaitacciya ce. Wannan ƙasar ba Saudiyya ba ce wadda ke da arzikin mai da za ta dogara da kanta, wannan ƙasa ce da ta dogara kacokan akan harkokin yawon buɗe idanu da kuma tallafi daga ƙasashen waje wanda aka rage shi a bara".

Jam'iyyun masu kishin addini sun amfana da zanga-zangar juyin juya halin da matasa suka gudanar, waɗanda kuma suka zama saniyar ware a harkokin siyasar. Bugu da ƙari janyewar Mohammed El-Baradei daga neman takarar shugabancin ƙasar alama ce dake nuni da wannan rauni a cewar Ronalad Meindrus.

"Babban taƙaici kuma koma baya ga 'yan gwagwarmayar juyin-juya halin shine mayar da su saniyar ware da aka yi a muhawarar harkokin siyasa, haka kuma janyewar El-Baradei daga takarar shugabancin ƙasa shi ma babban naƙasu ne da ke nuni da rashin tasiri".

Mawallafa: Diana Hodali/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani